Sojoji sun daƙile harin ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar sojin Najeriya ta 17 dake Katsina ta fatattaki wasu ‘yan bindiga masu tarin yawa bayan da suka yi yunƙurin kai hari a ƙaramar hukumar Charanci da ke jihar Katsina.

Rundunar ta samu nasarar daƙile harin ne bayan ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:20 na safe a ranar Talata da ta gabata, inda aka sanar da cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun taru a kusa da ƙauyen Kaɗɗanya da ke yankin.

Zagazola Makama mai sharhi kan tsaro ya bayyana cewa wani rahoton tsaro ya ce sojojin da ke sansanin FOB Raɗda sun gaggauta kai ɗauki inda suka mayar da martani bayan samun kiran gaggawar, tare da tattara dakarunsu inda suka nufi wurin da aka samu rahoton ganin wulgin ‘yan bindigar.

Sojojin sun yi aiki tare da jami’an rundunar yan sandan Najeriya da ke Kankia da Charanchi, da kuma jami’an tsaron Katsina C-Watch inda suka yi nasarar daƙile mummunan shirin ’yan bindigan na kai hari a ƙauyen.

Bayan kammala aikin, sojojin sun ci gaba da gudanar da sintiri a faɗin yankin tare da mamaye shi domin hana ’yan bindigar sake taruwa don kai wani sabon harin.

By ukarofi

Leave a Reply