Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
’Yan wasa takwas daga kwalejin ƙwallon ƙafa na Jihar Katsina sun bar Najeriya zuwa ƙasar Belarus, domin halartar horo a ƙungiyar FC Torpedo Zhodino da ke Minsk.
An zaɓi ’yan wasan ne a gasar Malam Dikko Raɗɗa Scouting Tournament da ta gudana a Katsina.
Shugaban kwalejin, Ahmed Mohammed, ya ce Gwamna Dikko Raɗɗa ya shirya gasar ne domin gano tare da bunƙasa ƙwararrun matasan ’yan wasan ƙwallon ƙafa daga ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Ya ce akwai yiwuwar wasu daga cikin ’yan wasan su samu kwangilar ƙwararru da FC Torpedo Zhodino-Belaz bayan kammala horon.
Ya ƙara da cewa wannan dama na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Raɗɗa na samar wa matasa hanyoyin shiga ƙwallon ƙafa ta ƙwararru da kuma tallata ƙwarewar ’yan Katsina a duniya.
