Kyautar lambar yabo daga Blueprint za ta ƙarfafa gaskiya da adalci yayin sauye-sauye a Zamfara, inji Gwamna Lawal

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya sanar da karɓar kyautar lambar yabo na Gudanar da Kuɗaɗen Al’umma bisa Gaskiya da Adalci ta jaridar Blueprint ta 2025, yana mai bayyana matakin a matsayin ƙarfafa wa ayyukan sauye-sauye da gwamnatinsa ke yi a jihar wajen tabbatar da tsare gaskiya da adalci da kuma gudanar da kuɗaɗen al’umma bisa tsari mai kyau.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Darakta-Janar na Yaɗa Labaransa, Nuhu Salihu Anka, yayin amsa wa saƙo daga hukumar gudanarwar ta jaridar Blueprint na sanar da shi cewa shi ne wanda ya yi nasarar samun kyautar.

Akan haka ne Lawal Dare ya bayyana godiyarsa ga hukumar gudanarwar Blueprint.ng bisa nuna gamsuwa da karrama ƙoƙarin da gwamnatin tasa take yi wajen sarrafa albarkatu da tsayar da gaskiya da adalci a harkokin Jihar Zamfara.

A cewar gwamnan, wannan karamci shaida ce ta cewa jajircewa kan aiki tuƙuru da ƙoƙarin gwamnatinsa wajen samar da sauye-sauye da nufin inganta lamuran shugabanci da tabbatar da an sarrafa dukiyar gwamnati bisa inganci.

Ya bayyana cewa, lambar yabon za ta ƙara wa gwamnatinsa ƙwarin-gwiwar cigaba da ƙoƙarin samar da gyare-gyare masu ma’ana da kafa gwamnati mai cike da gaskiya da adalci.

Ya ƙara da cewa, wannan kyauta ba iya karramawa ba ce kaɗai, saidai tana nuna hatta ƙoƙarin da jami’an gwamnatinsa da sauran masu ruwa da tsaki suke yi wajen bunƙasa harkokin gudanarwar gwamnati a jihar.

A ƙarshe, ya ce hakan zai taimaka wajen ƙarfafa musu a ayyukan gyare-gyare musamman akan lamuran da za su tabbatar da sarrafa dukiyar al’umma cikin inganci da adalci domin amfanin ‘yan jihar.

By Babaji

Leave a Reply