Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ozah Chinedu ɗan wasan ƙwallon kafa na ƙungiyar Katsina United ya rasu a yayin da yake buga wasan sada zumunta tsakanin ƙungiyar sa da ta Niger Tornadoes a filing wasa na Muhammadu Dikko a Katsina.
Dan wasan wanda tsohon ɗan wasan Kano Pillars ne kafin zuwan sa Katsina United ya gamu da ajalinsa a yayin da ana tsaka da wasa inda aka ga ya faɗi ƙasa.
Sanarwa daga sashin hulɗa da jama’a ƙungiyar Katsina United ta bayyana cewar an yi gaggawar kai shi asibitin ƙwararru na K_Dara a Katsina amma daga baya ya rasu.
Mutuwar ɗan wasan yazo wa ɗaukacin yan wasan ƙwallon ƙafar na ƙungiyar guda biyu da magoya bayan ƙungiyar Katsina United da hukumar ƙwallon ƙafa kafa ya jefa su cikin juyayi ganin wannan wasan sada zumunta shine wasan sa na farko a ƙungiyar da zai sharen fagen fara gasar firimya na wannan kakar.
Hukumar ƙwallon kafa na Katsina United ta ce har yanzu ba a san musabbabin mutuwar sa sai nan gaba ƙungiyar za ta fitar da ƙarin bayani.
