Kwamared Ɗahiru Maihula ya ƙudiri aniyar zama kakakin ƙungiyar matasan Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da zaɓen ƙungiyar matasan Nijeriya ta “Youth Assembly of Nigeria” (YAN) reshen jihar Kano ke cigaba da ƙaratowa, Kwamared Muhammad Ɗahiru Maihula ya ƙudiri aniyar tsaya wa takara domin neman kujerar kakaki a tafiyar jagorancin ƙungiyar.

Kwamared Maihula ya bayyana haka ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa da aka fitar a ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, 2026.

A cewarsa, ya ɗauki wannan mataki ne domin bayar da ga gagarumar gudunmawa ga harkokin shugabancin ƙungiyar bisa la’akari da cancanta da kuma wasu muƙamai da ya riƙe acikin YAN.

A baya, Kwamared Maihula ya riƙe muƙamai daban-daban a ƙungiyar, waɗanda suka haɗa da akawon mai tsawatarwa, daraktan yaɗa labarai, jami’in hulɗa da jama’a na reshen Kano, inda ya matuƙar bayar da gudunmawa bisa tsare gaskiya da adalci.

A cewarsa, a yanzu suna mayar da hankali ne akan muhimman al’amuran da suka shafi matasa musamman kan harkar shaye-shaye, dabanci, rashin aiki, ci-gaban shugabanci, da kuma shiga muhimman al’amura daga ɓangaren matasa.

Ya ƙara da cewa, zai cigaba da zama jajirtacce kuma mai biyayya wajen kare martaba da tabbatar da tsare gaskiya da adalci a shugabancin ƙungiyar da manufar duba maslahar matasa da ƙoƙarin samar da hanyoyin warware matsalolinsu, yana mai jaddada aniyarsa ta neman kujerar kakakin.

By Babaji

Leave a Reply