‘Yan bindiga 17 da ‘yan sanda 10 sun rasu yayin musayar wuta a Kebbi

Spread the love

Kimanin ‘yan bindiga 17 da ’yan sanda 10 ne suka rasa rayukansu yayin wata arangama a lokacin da wani gungun ’yan bindiga ke ƙoƙarin zuwa Jihar Kebbi daga Jihar Zamfara.

Haka kuma, rundunar ‘yan sanda ta ce fararen hula biyu sun rasu a yayin musayar wutar da aka yi tsakanin ’yan ta’addar da jami’an tsaro a yankin Rafin Makuku na Ƙaramar hukumar Sakaba da ke Jihar Kebbi a safiyar ranar Litinin.

Mazauna yankin sun kiyasta cewa ’yan bindigar sun kai kimanin 240 da ke kan babura sama da 200. Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun fito ne daga yankin Sangeko Gap da ke gundumar Ɗansadau a Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Wani mazaunin Makuku, Malam Musa Sani, ya ce ’yan bindigar sun rabu gida uku, inda suka yada zango a wani daji tsakanin Kakihum da Makuku, inda suka kwana kafin su nufi Maburya da safiyar Litinin.

Ya ce a yayin da ’yan bindigarsuke ƙoƙarin shiga garin ne suka ci karo da wani shingen binciken ’yan sandan kwantar da tarzoma inda aka yi musayar wuta tsakanin ɓangarorin.

Malam Musa ya yi zargin cewa ’yan bindigar sun kashe jami’an ’yan sanda 10 da fararen hula biyu, sannan suka kwashe bindigogin jami’an.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, DSP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar arangamar, yana mai cewa ya zuwa yanzu an tabbatar da kashe ’yan bindiga 17 da ake zargi ba.

Ya ce, “A safiyar yau (Litinin), jami’anmu sun tare, tare da yi wa wasu ’yan bindiga da ake ɗauke da muggan makamai ruwan wuta a yayin da suke tafiya tsakanin Zamfara da Kebbi ta yankin Rafin Makuku na Ƙaramar Hukumar Sakaba.”

A cewarsa, an kuma ƙona babura huɗu na ’yan bindigar a yayin arangamar, yayin da ake ci gaba da samun bayanai kan adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata.

Ya ce, “Abin takaici, mun rasa jaruman jami’an ’yan sanda 10 a arangamar, yayin da wasu biyu suka jikkata kuma suke karɓar magani.”

A cewarsa, abin da rundunar ta fi mayar da hankali a kai a yanzu shi ne tallafa wa iyalan jami’an da abin ya shafa, kula da waɗanda suka jikkata da kuma ci gaba da gudanar da samame domin cafke ’yan bindigar da suka tsere.

By Babaji

Leave a Reply