
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Martaba Sarkin Dutse a Jihar Jigawa, Dakta Hameem Nuhu Sanusi ya nuna damuwa akan yadda wasu da ba su samu ƙwarewa ba suke shiga harkar aikin jarida a Nijeriya, inda ya ce ayyukansu na haifar da cin fuska ga darajar fannin.
Manhaja ta ruwaito cewa, Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Ƙungiyar ‘Yan jarida ta Ƙasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya da mambobin Majalisar Zartarwarsa (NEC), waɗanda suka ziyarce shi a fadarsa a lokacin da suka je Dutse taron NEC da NUJ reshen Jigawa ta shirya.
Alhaji Hameem Sanusi ya ce, akwai matuƙar takaici a ce harkar jarida a yau ta faɗa hannun wasu marasa ƙwarewa da ke yaɗa ƙarairayi da labaran da ke haddasa tayar da zaune-tsaye acikin al’umma.
Akan haka ne Sarkin ya shawarci Shugaban na NUJ da ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi da zai taimaka wajen gano waɗanda “baragurbin” acikin harkar da kuma ɗaukar matakan da suka dace da su domin tsaftace harkar jarida.
Ya kuma bayyana cewa, a matsayinta na ginshiƙi na huɗu a tsarin gwamnatin dimukraɗiyya, NUJ za ta iya samarwa ko rushe dimukraɗiyya, yana mai bayyana harkar jarida a matsayin ginshiƙin samar da dimukraɗiyya mai ɗorewa a ƙasa.
A nasa jawabin, Kwamared Alhassan Yahaya ya ce sun je fadar sarkin ne da nufin nuna girmamawarsu a gare shi bisa goyon baya da gudunmawarsa ga harkokin NUJ a Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya, inda kuma suka naɗa sarkin a matsayin Uban Ƙungiya na NUJ reshen Jigawa.
