Akalla mutane 11 ne suka jikkata bayan wani ɗan bindiga ya buɗe wuta kusa da wata makarantar sakandare a birnin Turgutlu da ke lardin Manisa a yammacin Turkiyya.
Hukumomin ƙasar sun ce biyu daga cikin waɗanda suka jikkata suna cikin mawuyacin hali bayan harin da ya faru ranar Talata. An kuma kama wanda ake zargin bayan harin.
Rahotanni sun ce wanda ake zargin ɗalibi ne a makarantar, ko da yake binciken hukumomi kan ainihin abin da ya kai ga harin na ci gaba.
Harin ya sake dawo da hankalin jama’a kan matsalar hare-haren bindiga a makarantu a Turkiyya, bayan wasu hare-hare makamantansu da suka faru a ƙasar a watan Afrilu, waɗanda suka jawo sabbin matakan tsaro da ƙarin takunkumin mallakar makamai.
