Masoyin Aliyu Wadada ya raba wa mata injin niƙa a Lafia

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Wani matashin ɗan siyasa Abbas Zanwa wanda masoyi ne kuma wakilin yaƙin neman takarar mai neman kujerar gwamnan jihar Nasarawa na 2027 a Jam’iyyar APC wato Sanata Ahmad Aliyu Wadada daga gundumar Zanwa da ke ƙaramar hukumar Lafia ta Jihar Nasarawa ya raba wa mata injinan niƙa guda 10, domin taimaka musu wajen samun sana’o’in dogaro da kai.

Abbas ya bayyana cewa tallafin ya shafi mata ne musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ke ƙarƙashin gundumar Zanwa inda yace burinsa shi ne ganin mata sun rungumi sana’o’in dogaro da kai domin rage musu raɗaɗin talauci.

Ya ce, “Burina shi ne ganin mata sun rungumi sana’o’in dogaro da kai. Ina da burin taimaka wa mata da matasa domin kowa ya samu abin yi.”

A cewarsa a wannan karon ya raba injinan niƙa guda 10 ga mata tare da bai wa wasu mata 100 tallafin kuɗi na Naira 10,000 kowacce.

Abbas ya ƙara da cewa nan gaba zai duba wasu unguwanni domin gudanar da irin wannan tallafi, yana mai cewa irin waɗannan shirye-shirye zasu taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da rage raɗaɗin talauci a tsakanin al’umma.

“Abin da na yi ko da siyasa ce yana da kyau. Duk wanda yake neman ƙuri’a daga mutane ya kamata ya yi musu abin da zai taimaka musu su dogara da kansu,” in ji shi.

Da yake magana kan siyasar jihar Nasarawa Abbas Zanwa ya bayyana cewa shi masoyin ɗan takarar gwamnan Jihar Nasarawa 2027 a Jam’iyyar APC Ahmad Aliyu Wadada ne kuma yayi alƙawarin kawo masa ƙuri’u masu yawa a lokacin zaɓe.

Yace yana da yaƙinin cewa, insha Allah Ahmad Aliyu Wadada zai zama Gwamnan Jihar Nasarawa, tare da yin alƙawarin cewa gwamnatin sa za ta taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.

Abbas ya ce ya amince da tsarin siyasar Wadada musamman yadda ya ce ɗan siyasar ba ya cin mutuncin mutane kuma yana girmama jama’a tare da sanin ya kamata.

Ya bayyana Wadada a matsayin mutum mai kishin ci gaban al’umma yana mai cewa idan ya zama gwamna zai samar da yanayi na walwala da kuma damar samun ayyukan yi ga matasa da sauran jama’a.

Taron da aka gudanar a Kasuwar Alhamis ranar Lahadi maza da mata daga sassa daban-daban sun halarta ciki har da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa kamar ɗan takarar kujerar majalisan Lafia ta tsakiya Barrister Abubakar Imam Zanwa da babban mataimakin gwamnan Nasarawa Muhammad Abubakar da sauran masu riƙe da madafun iko.

Haka kuma an karɓi wasu waɗanda suka sauya sheƙa daga tafiyar tsohon sufeto janar na ƙasa Muhammad Adamu Abubakar zuwa tafiyar Ahmad Aliyu Wadada ɗan takarar jam’iyyar APC din a yayin taron.

Wakilin mu ya kuma ruwaito cewa kimanin mutane 145 ne suka sauya sheƙa zuwa goyon bayan Wadada daga gundumar Zanwa dake ƙaramar hukumar ta Lafia.

Jama’a da dama da suka halarci taron sun bayyana ra’ayoyinsu kan muhimmancin tallafa wa mata da matasa, tare da jaddada buƙatar samar da sana’o’in dogaro da kai domin inganta rayuwar al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply