Sufeto-Janar na ‘ yan sanda ya yi ta’aziyya ga iyalan ‘yan sanda da ‘yan ta’adda suka kashe a Kebbi

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi

Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu ya yi ta’aziyya ga iyalai da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kebbi dangane da rasuwar ‘yan sanda 10 a fagen fama.

Sufeto-Janar Disu ya turo wata tawaga mai karfi ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin Sufeto-Janar mai kula da dabarun yaƙi, DIG Umar Shehu Nadada, zuwa Birnin Kebbi domin gabatar da juyayinsa akan lamarin.

A sa’ilin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Nasir Idris a gidan gwamnati, DIG Nadada ya shaida masa cewar, ya zo Kebbi ne bisa umurnin IG Disu dangane da lamarin da ya yi sanadiyyar kisan ‘yan sanda guda 10 da ‘yan ta’adda su kayi.

Ya ce shugaban ‘yan sanda na ƙasa ya umurce shi da ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kebbi.

DIG Nadada ya bayyana cewar ‘yan sanda na iyakacin ƙoƙarinsu tare da haɗin-gwiwan sauran hukumomin tsaro wurin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, duk da yake akwai ɗan-gibi, amma za’a cike shi.

Ya sanar da cewar Sufeto-Janar ya amince a kafa wata sabuwar sikwadiron ta MOPOL a Kebbi, wadda za ta fara aiki ba da dade wa ba.

DIG Nadada ya ƙara da cewar hedikwatan ‘yan sanda ta ƙasa tana kuma ƙara ƙarfafa sauran rukunnai na ‘yan sanda, musamman waɗanda ake kira, ‘Tactical Teams’.

Yace ‘yan sanda ba za su yi sassauciba, rundunar za ta ƙara ƙaimi wurin fatattakar ‘yan ta’adda, sannan kuma waɗanda suka kai harin da ya yi sanadiyyar rasuwar ‘yan sandan 10, za su lashe-amansu.

A mai da jawabi da ya yi, Gwamna Nasir Idris ya yi godiya ga Sufeto-Janar Disu akan tausayawa da ya yi da kuma bada tabbacin kariya ga al’ummar Jihar Kebbi na rayukansu da dukiyoyinsu.

Kwamred Idris ya yi tir da abinda ya faru a ƙaramar hukumar Sakaba, a inda ‘yan sanda 10 suka mutu, a yayin da suke kare muradun ƙasar mu Najeriya.

Gwamnan ya bayyana cewar lamarin ya baƙanta ran gaba ɗaya al’ummar Jihar Kebbi ba ‘yan sanda kaɗai ba.

Yace gwamnatin Jihar za ta bada dukan gudunmawar da ta wajaba ga iyalan ‘yan sandan da su ka rasu.

Kwamred Idris yace, yana cikin muhimman tsare-tsaren gwamnati mai ci yanzu, ta bada kulawa ga dukan iyalan zarata na soja da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da suka mutu a wurin yaƙi, kula da rayuwarsu ta-yau-da-kullum.

Gwamnan ya nuna gamsuwa da irin jarumtakar da ‘yan sanda ke nunawa a fagen fama, sannan kuma ya gode ma sufeto-janar na ‘yan sanda dangane da yadda yake bada fifiko wurin kariyar al’ummar Jihar Kebbi.

By ukarofi

Leave a Reply