Gyaran farce bisa tsari: Karamar hanya da ke kare lafiyar ƙafa

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Akwai wasu abubuwa da muke yi a kullum waɗanda muke ɗauka ba su da wani tasiri mai yawa a rayuwa. Daga cikinsu akwai yadda muke kula da farcen ƙafa. Ga mutane da dama, gyaran farce wani ɓangare ne na tsafta kawai ko kuma gyaran kwalliya, amma masana lafiya sun nuna cewa yadda mutum yake yanke farcensa na iya taimaka masa wajen kauce wa matsalolin da kan jawo ciwo da wahalar jinya.

Kafa na ɗaukar nauyin jiki gaba ɗaya, kuma duk wata matsala da ta shafe ta na iya shafar tafiyar mutum da sauran harkokinsa na yau da kullum. Saboda haka, kula da ƙananan abubuwa kamar tsaftar farce da yadda ake gyara shi na da muhimmanci fiye da yadda wasu ke zato.

Daya daga cikin matsalolin da ake yawan fuskanta ita ce farce da ke shiga cikin fata, wadda likitoci ke kira ingrown toenail. Wannan matsala kan fara ne a hankali; mutum ya fara jin ɗan ciwo a gefen babban yatsan ƙafa, ko ya lura da ɗan kumburi. Amma idan aka yi watsi da ita, farcen da ke matsawa cikin fata na iya haifar da ciwo mai tsanani, kumburi da kuma kamuwa da cuta.

Masana sun bayyana cewa ɗaya daga cikin abubuwan da ke haddasa wannan matsala shi ne yadda ake yanke farce. Wasu mutane kan zurfafa yayinda suke yanke gefen farce sosai saboda ganin hakan ya fi kyau. Amma a ɓangaren lafiya, wannan hanya na iya sa sabon farcen da zai fito ya bi hanyar da ba ta dace ba, ya fara shiga cikin fata.

Saboda haka, ƙwararrun likitoci suka bada shawarar a rika yanke farcen ƙafa a mike, ba tare da zurfafa gefuna ba. Haka kuma ba a so a yanke shi ya yi gajarta ƙwarai, domin barin ɗan tsawon farce yana taimakawa wajen kare fatar da ke kewaye da shi.

Baya ga yadda ake yanke farce, tsaftar kayan aikin gyara ma na da matuƙar muhimmanci. Amfani da almakashi ko abin yanke farce da ba a tsaftace ba na iya zama hanyar shigar ƙwayoyin cuta cikin jiki, musamman idan an samu wan ƙaramin rauni a lokacin gyaran.

Haka kuma, masana sun yi gargadi game da cire fatar da ke gefen farce da ƙarfi. Duk da cewa wasu na ganin hakan yana ƙara kyau wurin, wannan fata tana da aikin kare yankin da ke kusa da farce daga ƙwayoyin cuta. Lalata ta na iya buɗe hanya ga kamuwa da cuta.

Ga masu fama da ciwon sukari kuwa, wannan kulawa ta fi zama wajibi. Saboda ciwon sukari kamar yadda yadda muka faɗa a makon baya, kan shafi yadda jiki ke warkar da raunuka, ƙaramar matsala a ƙafa na iya rikiɗewa zuwa babbar matsala idan ba a kula da ita da wuri ba. Shi ya sa ake shawartar su dinga duba ƙafafunsu akai-akai tare da neman taimakon likita idan suka ga wani canji.

A ƙarshe, gyaran farce daidai ba wai batun kwalliya ko tsafta kawai ba ne. Wata hanya ce ta kare lafiyar ƙafa da hana matsalolin da za su iya farawa daga wani ƙaramin kuskure. Sau da yawa, abin da mutum ke ganin ƙaramin aiki ne na yau da kullum na iya zama babban matakin kariya ga lafiyarsa.

By ukarofi

Leave a Reply