(Ci gaba daga makon jiya)
Daga MUKHTAR YAKUBU
“Shekara ta takwas kenen ina sana’ar karuwanci amma ba abinda na amfana da shi,” in ji wata karuwa
Da yake ba wannan ne ya fi damu na na sani ba, nan take sai na katse ta da tambayarta, duk tsawon shekarunta da take wannan sa’ar, wacce riba ta taɓa samu kuma wacce wahala ta taɓa fuskanta, kuma ko tana tunanin barin sana’ar nan gaba idan ta samu kudi ko mijin aure?
Sai ta ce, “Ni dai yanzu ina jin ina cikin shekaruna na takwas kenen a cikin wannan sana’ar ta karuwanci, kuma har yanzu ni dai babu abin da na amfana da shi idan banda shaye-shaye da na koya da kuma rashin ganin mutuncin kowa.
Ba na mantawa na taɓa samun wani saurayi a gidan dambe ya ɗauke ni kwanan gida, muka tafi bayan ya bugar dani ya kwana lalata dani har gari ya waye, da safe kuma ya gayyato abokanen sa uku suma ko karyawa ban yi ba suka auka mini, suka gudu suka bar ni masu otel suka kamani suka ce dole ni zan ba su kuɗin dakinsu a wannan dalilin sai da na yi kwanaki 20 a gidan fursina kafin na fito.
Game da ko ina da niyyar barin wannan sana’ar, gaskiya ina da niyar bari idan na samu halin bari, saboda ni yanzu bani da kuɗi, babu saurayi na kirki da zai aure ni, kuma ni ba zan iya komawa gida na zauna ba, don haka gani nan dai sai abin da Allah ya yi ‘ kawai, amma a zahiri babu daɗi a wannan sana’ar sai baƙar wahala kawai.”
Da hakan ta kammala bani labarin wuyar da ta sha a sana’ar tata ta karuwanci.
Ita kuwa Jamila wacce ta ce sunanta na asali kenan kuma ba ta tsoron na rubuta, ta soma ne da bani nata labarin da cewa, ita ba ta zuwa ko ina yawon neman abokan sana’ar zinar ta, sai dai ita ta kware ne a tsayuwa a kan hanya idan dare ya yi domin a zo a ɗauke ta, kuma a nan ne take samun abokanen zinar ta, wani lokacin idan ta dace ta samu na kirki wani lokacin kuma ta sha ɗan karen wahala.
“Kin ganin nan, na daina bin maza gidansu, da nakan bi namiji gidansa idan ya ɗauke ni, amma tun da na sha da kyar a hannnun wani dan yankan kai na daina amincewa na bi maza gidajensu. Kin san ni na fi kwarewa ne na tsaya a kan hanya idan dare ya yi ina jiran wanda zai dauke ni, kuma babban haɗarin dake cikin irin wannan karuwancin shi ne na rashin sanin mai ɗaukar ki.
To a haka ne ranan na samu wani mutum ya nuna yana sona bayan na shiga motarsa ya ce na fito da nonuwana ya gani, ya taɓa duwawuna ya ce mini na yi daga nan kuma ya kaini naci abinci mai kyau mai tsada, sannan ya umurce ni idan na amince yana buƙatar mu wuce gidansa, ni kuwa na amince ganin sa babban mutum mai kuɗi kuma ga kamala. Tabbas na gane inda muka dosa domin hanyar gidan nasa hanya ce da duk wanda yake garin (ta faɗi sunan garin ) ya san wajen har muka shiga ƙofar farko ta gidan ina cikin hankalina, amma kuma abin mamaki muna shiga kofar karshe ta cikin gida bayan na ga wasu kartin sun buɗe kofar gidan kawai sai na fita daga cikin hayyacina. Na ci gaba da bin sa har muka shiga wani katon falo, shigar mu ke da wuya na fahimci cewa na shiga hannu ɗan yankan kai.”
Jamila ta ci gaba da bada labarin da cewa, ” Bayan mun shiga falon ne ya umurce ni da na cire takalma na, na kuma tuɓe na yi tsirara, daga nan ne kuma na ga wasu alamu irin na kawunan mutane, nan take na fashe da kuka tare kuma da rokon sa ya taimaka mini ya yi mini rai, amma ya ce sam sai na bi umurninsa na tuɓe tsirara haihuwar uwata na zauna a kan wata kujera da aka lullube ta da wani jan kyalle na buɗe kafafuna.
Daga nan dai na shiga wani yanayin da hankalina ya gushe ta yadda ban san abin da ya ci gaba da faruwa ba. Kawai dai na farka ne na ganni a kwance a gefen titi mutane sun kewaye ni suna kallo na Aka ɗauke ni aka kai ni asibiti.
Bayan na samu sauƙi ne na dawo inda nake amma dai ban san abin da ya faru da ni ba a gidan bayan hankali na ya gushe, kuma ban san yadda aka yi na fita ba.”
