Katsina United ta sake tabbatar da mutuwar ɗan wasanta da aka ce ya farfaɗo a ɗakin ajiyar gawarwaki

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United da masu sha’awar ƙwallo a jihar Katsina sun shiga jimami bayan da ƙungiyar ta sanar cewa sabon ɗan wasanta, Ozoh Chinedu, wanda a baya ya taka leda a Kano Pillars, ya rasu.

Rahotanni sun ce Chinedu ya rasu a safiyar Talata, 11 ga Agusta, 2026, bayan samun matsalar lafiya yayin wasan sada zumunta da Katsina United ta yi da Niger Tornadoes a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina.

A cikin wata sanarwa da sashen yaɗa labarai na Katsina United ya fitar, an bayyana cewa an ba ɗan wasan agajin gaggawa kafin a garzaya da shi zuwa asibitin K-Dara Specialist Hospital domin samun kulawar likitoci.

Sai dai duk da ƙoƙarin da aka yi na ceto rayuwarsa, Chinedu ya rasu a asibitin.

Katsina United ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokan wasansa, abokansa da ɗaukacin masoya ƙwallon ƙafa, tare da addu’ar Allah ya ba waɗanda abin ya shafa ƙarfin gwiwa da haƙurin jure rashin.

By ukarofi

Leave a Reply