Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Shirin inganta Ilimin ‘yan matan Zamfara AGILE, ya fara horo na kwana biyu yau Talata, a Taula Apartment da ke Gusau ga ‘yan kwangila, ma’aikatan gini, injiniyoyi da kuma masu ba da shawara kan kula da muhalli.
Bitar ta mayar da hankali kan aiwatar da shirye shiryen gudanar da muhalli da zamantakewa, ESMPs, a fadin wuraren aikin AGILE a jihar.
Da yake buɗe taron bitar, mataimakin mai gudanar da ayyukan hukumar ta AGILE a Zamfara, Dr. Salisu Dalhatu ya ce manufar ita ce a wayar da kan mahalarta bitar game da haɗurran muhalli da ke da alaƙa da gina makarantu da gyaran su, da kuma gano hanyoyin da suka dace, na musamman don magance su.
Ya jaddada cewa saboda ayyukan AGILE sun bambanta da al’umma, rage tasirin ba zai iya zama na gama gari ba.
Ya bayyana cewar ‘yan kwangila dole ne su daidaita ayyuka bisa ga yanayin gida, tsarin al’umma, da barazanar tsaro don kare ɗalibai, ma’aikata, da al’ummomin da ke karbar baƙuncin su.
Horarwar ta shafi muhimman fannoni guda huɗu na ESMP. Mahalarta suna koyo game da kare muhalli kamar sarrafa ƙura, sarrafa sharar gida, hana zaizayar ƙasa da kuma kare magudanan ruwa.
Ana kuma horar da su kan lafiya da aminci a wurin aiki, gami da amfani da kayan kariya na sirri (PPE) da kuma rigakafin haɗurra.
A ɓangaren zamantakewa, Dakta Dalhatu ya ce taron bitar ya tabo batun hulɗar al’umma, kare yara, rigakafin cin zarafi bisa ga jinsi da kuma tsaron ‘yan mata matasa.
Yana mai jaddada cewar, horon ya shafi sa ido da bayar da rahoto, tare da mai da hankali kan takardu, duba bin ƙa’idodi da kuma rawar da masu ba da shawara kan sa ido ke takawa.
Aikin AGILE, wanda bankin duniya da Gwamnatin Tarayya ke tallafawa, yana da nufin faɗaɗa damar samun ilimin sakandare ga ‘yan mata a Zamfara ta hanyar ginawa da gyara makarantun da suka dace, tare da tabbatar da cewa duk wani aiki ya cika ƙa’idodin ƙasa da manufofin kare lafiyar yara na bankin duniya.
