Matashi ya haddace Alqur’ani a lokacin da yake zaman gidan yari

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wani matashi mai suna Yusuf Shu’aibu, ɗan ƙaramar hukumar Mai’adua da ke Jihar Katsina, ya haddace Alqur’ani mai girma a lokacin da yake zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu a Daura.

Yusuf ya fara karatun Alqur’ani ne a ƙarqashin ƙungiyar Ansarul Islam Da’awa, wadda ke ƙarqashin jagorancin Malam Mujtaba Tukur.

Da yake bayyana yadda zaman gidan yarin ya shafe shi, Yusuf ya ce wannan lokaci ya taimaka masa wajen barin wasu munanan ɗabi’u, ciki har da shaye-shaye, tare da mayar da hankali kan karatun Alqur’ani mai girma da sauran littattafan addini.

Matashin ya kuma bayyana cewa mahaifiyarsa ta sanar da shi cewa ta yafe masa a duniya da lahira, lamarin da ke nuna muhimmancin yafiya da damar da mutum ke da ita na sauya rayuwarsa.

An gudanar da walimar kammala haddar Alqur’anin ne a ranar da Yusuf ya kammala wa’adin zaman gidan yarinsa, tare da haɗin gwiwar hukumar gidan yarin da ƙungiyar Ansarul Islam Da’awa.

Haka kuma, wasu daga cikin mutanen da ake tsare da su a gidan yarin sun haddace juz’i goma ko fiye na Alƙur’ani, yayin da suke ci gaba da karanta littattafan addini.

Wannan lamari ya nuna yadda samun damar karatu da koyon addini zai iya taimaka wa wasu mutane wajen sauya rayuwarsu, har ma a lokacin da suke fuskantar ƙalubalen zaman gidan gyaran hali.

By ukarofi

Leave a Reply