‘Yan sanda ceto ɗan shekara 10 bayan kama mutum biyu bisa zargin garkuwa a Sakkwato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Sakkwato ta yi nasarar cafko wasu mutum guda biyu bisa zargin su da hannu a ayyukan garkuwa da mutane a tisaye mabambanta da kuma ceto wani yaro ɗan shekara 10 da aka yi zargin an sace shi ne a jihar.

Rundunar ta ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, mai suna Abdullahi Buba da aka sani da “Osho”, mamba ne a wata sananniyar dabar garkuwa a sassan Jihar Sakkwato.

Kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce an kama Buba ne a ranar 8 ga Agusta yayin wani samame da jami’an tsaro suka ƙaddamar a yankin ƙauyen Tudun Doki da ke Ƙaramar Hukumar Gwadabawa. An gudanar da atisayen ne da misalin ƙarfe 2 na rana bayan samun wani bayanin sirri.

Bincike a karon fari a cewar ‘yan sandan, sun nuna cewa Buba da na hannu a ayyukan garkuwa da mutane da kuma karɓar haramtattun kuɗaɗen tara daga wasu ƙauyuka a ƙananan hukumomin Gwadabawa, Kware da kuma Gada.

Haka kuma, rundunar ta ce yana kuma taimaka wa masu bincike bin diddigin sauran mambobinsu da ake nema ruwa-a-jallo.

A wani atisayen kuwa, jami’an ‘yan sanda sun ceto wani ɗan shekara 10 mai suna Muhammad Sufiyanu bayan an ruwaito ceto ya ɓata a garin Gidan Madi da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza.

Kawun yaron, Sani Ibrahim ne ya ruwaito wa ‘yan sanda batun ɓatan nasa tun a ranar 11 ga Agusta.

By Babaji

Leave a Reply