Daga UMAR GARBA a Katsina
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta kama wata budurwa kan zargin koya wa wasu yara maza yadda zasu riƙa aikata lalata da junansu a ƙaramar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina.
Bayanin haka na cikin wata sanarwa da hukumar Hisbah ta jihar Katsina, reshen Dutsinma ta fitar.
A cewar sanarwar, hukumar ta kama wadda ake zargin bayan samun rahoton lamarin daga ofishin yankin Ƙadangaru da ke ƙaramar hukumar ta Dutsinma.
Sanarwar ta ce, kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Malam Shafi’u Ibrahim, ya karɓi rahoton tare da ɗaukar matakan bincike, inda jami’an hukumar P.I.H. Hamisu Sani da sauran jami’an hukumar suka gudanar da binciken farko.
Ya ce, binciken farko ya nuna cewa ana zargin budurwar da ɗaukar yaran da kuma koyar da su wannan mummunar ɗabi’a, inda hukumar ta ce binciken zai ci gaba bisa doka domin kare yaran daga duk wani nau’in cin zarafi ko lalata.
Hukumar Hisbah ta jaddada cewa kare yara da tarbiyyarsu na daga cikin manyan nauyin da ke kanta, tare da bayyana cewa za ta ɗauki matakan da suka dace bayan kammala binciken.
