Rasuwar wacce nake so ce sanadin fara waƙa ta – Halifa Maiyabo 

Daga IBRAHIM HAMISU 

Ahmad M. Ahmad da a ka fi sani da Halifa Maiyabo matashin mawaƙi ne, wanda ya ke tasowa a duniyar waƙoƙi. A tattaunawarsa da Wakilin Blueprint Manhaja, IBRAHIM HAMISU, a Kano za ku ji taƙaitaccen tarihin rayuwarsa da kuma yadda a ka yi ya samu kansa a harkar waƙa. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Ka gabatar mana da kanka?

HANIFA MAIYABO: Sunana Ahmad M. Ahmad amma an fi sani na da Halifa Maiyabo.

Ba mu taƙaitaccen tarihinka?

An haife ni a sabon titi na Dandago cikin birnin Kano, daga bisani yanayi na rayuwa ya sa mu ka koma unguwar Rijiyar Zaki, inda na yi primary school a Ɗorayi Babba, kazalika na yi secondary school a Ɗorayi Babba, to daga nan na tsaya ban samu damar cigaba ba, sai dai ina saran zan cigaba in sha Allah nan ba da daɗewa ba.

Ta yaya ka samu kanka a harkar waƙa?

Na fara waƙa ne ta sanadiyyar wata baiwar Allah mai suna Khadija wacce nake tsananin son ta, mun shaƙu sosai dan bama yini ba mu yi waya sau uku a rana ba, to a lokcin na fara rubuta mata waƙa, amma Allah ya mata rasuwa Allah ya jikan ta.

Da wacce waƙa ka fara?

Na fara ne da waƙar soyayya, daga baya kuma sai na riƙa yin waƙoƙin begen ma’aiki S.A.W. amma a yanzu na fi yin waƙoƙin nanaye.

Waƙoƙi nawa ka yi a ɓangaren bege?

Za su yi kamar guda huɗu zuwa biyar.

Ta ɓangaren waƙoƙin nanaye kuma fa sun kai nawa?

Sun kai guda 12.

Mene ne bambancin da ke tsakanin waƙoƙin bege da na nanaye?

Bambancin a fili yake shi bege ana yinsa ne don Annabi SAW. Shi kuma nanaye kuma abu ne da ya shafi lamarin duniya da sanya nishaɗi ga al’umma. 

Daga lokacin da ka fara zuwa yanzu waɗanne irin nasarori za ka iya cewa ka samu?

Suna da yawa gaskiya, amma babbar nasarar da na samu ita ce mutane, domin mutane suna fuskantar mai nake yi kuma suna saurarena.

Ƙalubale akwai ko babu?

Ba za a rasa ba, amma Alhamdu lillahi.

Wane ne mai gidanka?

Gaskiya ba ni da maigida sai dai abokan aiki.

Waɗanne waƙoƙi ne duniya ta fi sanin ka da su?

Waƙoƙina da aka fi sani da su kai guda biyar ne, na soyayya da na bege, da suka haɗa da Mama, Daidai ni, Masoyiya, da kuma na addini; Ta daban ce, Mu’asumiyya.

Ko za ka iya tuna wata waƙa da ta ba ka wahala wajen rubutawa ko rerawa?

Wata waƙar biki ce ta ba ni wahala sosai saboda a lokacin ban goge ba kuma ga shi ta zo min a lokacin ban shirya ba, kuma a ƙurarran lokaci, domin ana gobe za ayi bikin aka sanar da ni, waɗannan dalilan ya sa waƙar ta ba ni wahala. 

Wacce waƙa ce bakandamiyarka?

Waƙar Mama.

Salon wane mawaƙi ka ke amfani da shi?

Suna da yawa, amma waɗanda na fi ɗauka salon su su ne Umar M. Sharif da Hamisu Breaker.

Mene ne burinka a nan gaba?

Burina na kafa gidauniyar tallafawa marayu, ta yadda zan taimake su har su ji kamar ba su rasa komai ba.