Ba zan iya auren duk wanda ba ya son harkar fim ba – Asmee Wakeel

Daga MUKHTAR YAKUBU 

A wani saƙo da ta saki mai kama da mayar da martani, Jaruma a masna’antar finafinan Hausa ta Kannywood, Asmau Wakili wadda aka fi sani da Asmee Wakili, ta bayyana cewar ita sam ba za ta iya zama da duk wanda ba ya son sana’arta ta fim da take yi ba.

Jaruma Asmee Wakeel ta bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, wanda hakan ya sa ake ganin mayar da martani ne ga mutanen da suke kyamatar auren ‘yan fim tare da jifan su da kalamai marassa daɗi a game da sana’ar su ta fim.

Domin kuwa wasu na kallon sana’a fim a matsayin wata sana’a da ba za su iya zaman aure da duk wata jaruma wanda take cikin harkar ba, wannan ya sa jarumar a matsayin ta na ‘yar masana’antar ta fito fili ta yi suka a kan hakan tare da yin kira ga abokan sana’ar ta da su ma su fito su nuna cewa suma haka abin yake a wajensu domin kuwa kowa tashi ta fisshe shi.

Asmee Wakili jarumar Kannywood ce wacce ta shahara a wannan kafa musamman fannin raye-raye inda take fitowa a manyan finafinai tana tiƙar rawa tare da abokan aikinta, hakan ya sa ta tara ɗimbin masoya masu sha’awar kallon waƙoƙin da take fitowa a cikinsu.