Emefiele ba ya bayar da kwangila sai da cin hanci, in ji shaida

Daga BASHIR ISAH

Mutum na biyu da ke ba da shaida a kan shari’ar da tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ke fuskanta, ya bayyana wa Kotu ƙarara cewa lallai Emefiele ba ya ba da kwangila ba tare da ya karɓi cin hanci ba.

John Ayo wanda ya kasance tsohon Darakta na Sashen Labarai na CBN, ya bayyana haka ne ga Babban Kotun da ke zamanta a Ikeja, Jihar Legas.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake ba da shaida a gaban Alƙali Rahman Oshodi yayin zaman da kotun ta yi a ranar Litinin.

Emefiele na fuskantar shari’a ne kan zargin yin amfani da ofishinsa wurin aikata ba daidai ba da kuma kaɓar cin hancin da ya kai Dala biliyan 4.5 da kuma Naira biliyan 2.8.

A cewar Ayoh, “Yadda ya kansace yana gudanar da aikinsa ke nan, sai ya karɓi cin hanci kafin ya ba da kwangila.”

Shaidar ya yi wa kotun bayani dalla-dalla yadda ya wakilci Emefiele wajen karɓa masa cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.

Ya ce cin hancin farko da Emefiele ya karɓa shi ne $400,000 wanda wani hadiminsa, John Adetola, ya zo gidansa de ke Lekki ya karɓa wa Emefiele ɗin.

Ya ci gaba da cewa, kuɗi na biyun da ya karɓa wa Emefiele $200,000 wanda wani ɗan kwangila ya kawo hedikwatar CBN a Legas.

Ya ƙara da cewa, a mokacin da ya je miƙa Emefiele kuɗin a ofishinsa bayan da ya karɓa daga hannun ɗan kwangilar da ya kawo, a nan ya tarar da wasu shugabannin bankuna da dama ciki har da marigayi Hebert Wigwe, waɗanda ke zaman jiran ganawa da Emefiele ɗin.