Tare da NASIRU ADAMU
In dai Isra’ila ta ce za ta kai hari to a jira lokaci sai ta kai ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar mutuwar waɗanda ba su da laifin komai. Kazalika ƙasar ta Yahudawa da ta mamaye ƙasar Falastinawa kan samu goyon baya ne na kai tsaye ko ta bayan fage daga manyan ƙasashe musamman na yammancin duniya.
Isra’ila kan iya aibata hukuncin kotun duniya kuma ta kwana lafiya. Haqiqa akwai wasu ƙasashe da in sun gwada kaɗan daga ɗabi’un Isra’ila za su iya fuskantar wariya da ma kai yaqin ƙasashe na taron dangi. A ɓangaren Isra’ila duk hari ko martani mai tsauri da ta kai na tafiya salun-alun a matsayin kare kai.
Wannan yaƙi ma na Gaza da ya faro daga 7 ga Oktobar bara ya na tafiya ne zuwa yanzu a matsayin murqushe ƙungiyar Hamas. Duk da labari ya zo cewa Hamas da ta kutsa yankin Isra’ila ta kashe kimanin mutum 1, 200 amma ramuwar kare kan Isra’ila ta kashe fiye da Falastinawa 35, 000 kuma akasari mata da ƙananan yara kuma har yanzu zubar da jini na gudana. Isra’ila dai sam ba ta amincewa da cewa ita ta tunzura Hamas wajen kai hari don yadda ta ke yi wa Falastinawa kisan ɗauki daidai da kuma kama dubban Falastinawa da ta zuba a gidajen yarin ta.
Kisa a wajen Isra’ila da sunan kare kai ba ma wani babban lamari ba ne don ya kan faru a kusan kullum. Duk wata yarjejeniya ta haɗin kai da wasu ƙasashen Larabawa kan ƙulla da Isra’ila ba sa hadawa da bin kadun Falasɗinawa.
Tamkar a ce kawo batun ‘yancin Falasɗinawa ko kafa ƙasar Falasɗinu wasu batutuwa da sai Mahdi za a iya tavo su.
Gwamnatin Isra’ila ta Firaminista Benjamin Netanyahu ba ta sha’awa ko na miskala zarratin a yi maganar. Wannan ya sa kiraye-kirayen da ƙasashen Larabawa ke yi na kafa qasar Falasdinu mai helkwata a gabashim birnin Kudus ya zama na fatar baki.
In za a tuna a zamanin mulkin tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana kaurar da ofishin jakadancin Amurka na Isra’ila daga Tel’Aviv zuwa birnin Kudus don marawa mamayar Isra’ila baya. Kuma son samu a lokacin da Trump ya jagoranci sulhunta wasu qasashen Larabawa da Isra’ila da taken “Yarjejeniya Ibrahim ” don haɗa kan dangogi ko waɗanda ke alakanta kan su da Annabi Ibrahim; sai a ba wa Falasdinawa ‘yancin su a zauna lafiya. Sai dai ba haka a ke so ba.
Duk burin Isra’ila shi ne yankin Falasɗinawa ya ci gaba da zama qarqashin mulkin mallakar Isra’ila kuma ta nan Yahudawa su cigaba da samun matsugunai a sauran yankunan Falasɗinawa.
A ɓangaren shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ma bai wuce ya riƙa nuna takaici ba don kamar ba wani mataki da zai iya ɗauka.
Kazalika gwamnatin sa ma na caccakar Hamas da nuna ita ta yi tsokana ko ta jawo sabuwar gagarumar fitinar. Hakan ba zai zama da mamaki ba don bambancin da ke tsakanin sassan biyu a siyasance.
A gaba ɗaya a wakilcin diflomasiyyar Falasɗinawa a duniya ba nuna wani bambanci sai kamfen na tabbatar bin kadun Falasɗinawa. Samun barakar manufa ta cikin gida a tsakanin Falasɗinawa kan iya kawo gugar zana lokaci-lokaci a tsakanin Hamas mai mulkin Gaza da babbar gwamnatin Falasɗinawa ta birnin Ramallah.
Babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da a ba da dama Falasdinu ta zama cikakkiyar kasa mai ‘yanci.
Zauren ya kaɗa ƙuri’a da gagarumar nasara don amincewa da ‘yancin ƙasar Falasdinawa. Zauren ya amince Falasdinu ta zama ƙasa ta 194 a jerin membobin majalisar.
A yanzu dai Falasɗinu na matsayin mai sa ido a majalisar ba tare da ‘yancin kaɗa ƙuri’a ba.
Babban zauren ya buƙaci kwamitin sulhu ya sake bita kan kafa ƙasar Falasɗinu.
A baya dai Amurka ta hau kujerar na ƙi a kwamitin sulhu mai tasiri lokacin kaɗa ƙuri’a don neman kafa ƙasar Falasɗinawa.
Samun wannan matsaya ta bai ɗaya nasara ce ga Falasɗinawa duk da ba lallai ne har halin da a ke ciki Amurka ta bar ƙudurin ya tsallake a kwamitin sulhu ba.
Duk da haka a iya sa rai don yadda Amurka kan gargaɗi wuce gona da irin Isra’ila amma Netanyahu kan yi biris da hannunka mai sanda da a ke yi ma sa.
Akwai buƙatar a ja hankalin Amurka ta mara baya ga kafa ƙasar Falasɗinawa tun da wannan tsohon zance ne da a ka yi amanna zai zama maslaha ta rage fitinar gabar ta tsakiya.
Ba mamaki kuma Amurka na da muradi a wannan karon na yin zagi wajen samun kafa ƙasar Falasɗinawa. Idan a ka kafa ƙasar Falasɗinawa za ta iya samun duk kariya ta diflomasiyya.
Ƙasar Isra’ila ta yi biris da kandagarkin ƙasashen duniya ta aukawa Rafah. Tankunan yaƙin Isra’ila sun shiga gabashin garin Rafah da ke kudancin Gaza kan iyaka da Masar.
A Rafah akwai fiye da Falasɗinawa miliyan ɗaya mazauna Gaza da ke samun mafaka sanadiyyar ruwan boma-boman Isra’ila a arewacin Gazan.
Tuni a ke jin ƙarar tada boma-bomai kan gidaje da kuma arangama da sojojin na Isra’ila.
Wannan ya nuna ƙarara tabbatar barazana ga rayukan fararen hula a garin yayin da Isra’ila ke cewa ta na farautar ‘yan HAMAS ne.
Ƙatar ta ce kutsawar Isra’ila garin Rafah ya kawo matsala a yarjejeniyar tsagaita wuta da a ke yi birnin Alkahira.
Yanzu dai an shiga rudani da rashin sanin tabbas biyo bayan wannan mataki na Isra’ila da hatta Amurka da ke mara ma ta baya ke togaciyar kar ta aukawa Rafah.
Tamkar dai Isra’ila na da burin murƙushe ba wai kawai HAMAS ba hatta Zirin na Gaza wanda hotunan tauraro ke nuna kashi 75% na gine-ginen sa sun zama tarin ƙasa don boma-bomai da Isra’ila ta sauke.
Shugaban Amurka Joe Biden ya gargaɗi Isra’ila da sam kar ta kai mummunan harin nan kan Rafah don illar hakan kan fararen hula.
Biden ya yi gargaɗi cewa matuqar Isra’ila ta bijire to Amurka za ta daina tura ma ta makamai.
Biden ya amince cewa da makaman Amurka ne Isra’ila ke amfani wajen kashe Falasɗinawa a yaƙin Gaza.
Kai farmakin na Isra’ila na nuna yin biris da gargaɗin duniya da Isra’ila ke cigaba da yi kuma cikin girman kan ba wanda zai iya taka ma ta birki. Isra’ila ta nuna za ta yi wannan yaki na Rafah ba tare da mara bayan Amurka ba.
Gabanin rikicewar lamarin nan ƙasar Masar ta buƙaci ɓangarori biyu a yaqin Gaza su tabbatar da nasarar yarjejeniyar tsagaita wuta.
Wannan na zuwa ne bayan wata 7 Isra’ila na ruwan wuta kan Gaza.
Nasarar da a ka samu ta amincewar Hamas kan yarjejeniyar da Masar da Katar su ka jagoranta ta kawo kwarin gwiwar amincewar ɓangarorin biyu na kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya.
Shugaban Masar Abdelfatah Elsisi ya ce ya na zuba ido kan duk halin da a ke ciki don samun karɓuwar tattaunawar da a ke yi a birnin Alkahira.
Ƙarin bayani kan yanayin da Gaza ke ciki a bitar na’ura na gano 75% na gine-ginen Gaza sun rugurguze sanadiyyar boma-boman Isra’ila; na kawo takaicin da ko an dakatar da yaƙin Gazawa za su kasance a ciki na rashin matsuguni.
Wannan ma a na ganin ya fi abun da ya samu birnin Dresden na Jamus a ƙarshen yaqin duniya na biyu.
Mafi munin ruguje gidajen Gaza ya auku ne a wata 3 na farkon yakin.
Isra’ila ta ragargaza asibitoci 5 da yanzu sai dai a gina wasu a zirin. Yanzu ga shi Isra’ila ta shiga harbe-harbe a Rafah wanda haƙiƙa hakan babbar barazana ga rayuwar dubban rayukan Falasdinawa da su ke fake a garin don yadda Isra’ila ta ke bin su da kisa a arewacin Gaza.
Isra’ila ce fa ta umurci Falasɗinawa su bar arewaci su yiwo kudancin Gaza amma haka ta biyo su kudancin da hare -hare. Sai da fa a ka haƙiƙance ba wani tudun mun tsira a yaƙin Gaza kakaf.
‘Yan tawayen houthi da ke mulkin manyan yankunan Yaman sun ayyana samun nasara kan sojojin ruwan Amurka a tekun Meditireniya.
Ƙungiyar ta lashi takobin cigaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka da Burtaniya kan yaƙin Gaza.
Kammalawa;
A zahiri dai yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas ta samu tangarɗa bayan kutsawar sojojin Isra’ila garin Rafah. Duk da haka Masar da Katar har ma da Amurka ka iya ƙara matsa ƙaimi don dakatar da wannan yaƙi da zummar ƙare zubar da jinin fararen hula.
Ma’ana ba za a yar da ƙwallon mangoro kan neman maslaha ba don abu ne da ya shafi mutum miliyan 1.2. Tun da a ka fara yaƙin mu ke ganin hotunan jarirai an kashe su. Wato ba ma a na maganar kananan yara kaɗai ba jarirai a ke kashewa. Kotun duniya ma ta na iya ƙoƙarin ta kan lamarin na Gaza.
Ya na da kyau duk ƙasashen duniya balle ma Larabawa su dage wajen yin caa a kan Isra’ila ta dakatar da wannan yaƙin da Afurka ta kudu ta tabbatarwa duniya cewa kisan ƙare dangi ne.