Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Mai bai wa gwamnan Jihar Katsina shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana, ya jaddada muhimmancin farfaɗo da shirin Community Development domin ƙarfafa ci gaban al’umma a dukkan ƙananan hukumomin jihar.
Hon. Safana ya bayyana hakan ne lokacin da shugabanni da mambobin ƙungiyar daraktocin Ilimi da ci gaban al’umma (ESD) na ƙananan hukumomi suka kai masa ziyarar neman goyon baya a ofishinsa.
Ya ce sashen ayyuka zai samar da kayan aikin Community Development domin rabawa ƙananan hukumomi, inda ya bayyana cewa za su kasance ƙarƙashin kulawar sassan ESD.
Ya kuma yi bayani kan batutuwan da suka shafi COHENSS da kuma harkokin Community Development, tare da buƙatar ma’aikatan ESD su rinƙa saɓunta iliminsu kan aikin su, su ƙarfafa haɗin gwiwa da shugabannin ƙananan hukumomi da sauran ma’aikata, tare da gudanar da ayyukan su cikin adalci da ƙwarewa.
Tun da farko, shugaban ƙungiyar kuma daraktan ESD na ƙaramar hukumar Kankia, Alhaji Garba Sani Mawashi, ya gabatar da muhimman ƙalubalen da suka shafi COHENSS da sauran ayyukan jin daɗin al’umma, yayin da sauran mambobin ƙungiyar suka gabatar da batutuwan da suke buƙatar kulawa domin inganta ayyukan sassan ESD a faɗin jihar.
