Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fara tattaunawa da ’yan kasuwa da kamfanonin Nijeriya da Chana domin nemo hanyoyin magance matsalolin biyan kuɗi tsakanin ƙasashen biyu, ƙarfafa hulɗar bankuna da inganta hada-hadar kuɗi a tsakaninsu.
Matakin na da nufin gano matsalolin da ke kawo cikas ga hada-hadar kasuwanci, inganta damar samun ayyukan kuɗi da hanyoyin tura kuɗaɗe, tare da buɗe ƙarin damammakin zuba jari ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwar tsarin kuɗi na tattalin arzikin ƙasashen biyu.
Wannan na ƙunshe ne cikin sakamakon wani babban taron tattaunawa tsakanin ’yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a harkokin kuɗi, wanda aka gudanar a otel ɗin Pan Pacific da ke birnin Beijing na ƙasar Chana, ranar Laraba, 21 ga Oktoba, 2026. A cewar babban bankin, tattaunawar ta mayar da hankali kan inganta tsarin biyan kuɗi tsakanin ƙasashen biyu, ƙarfafa haɗin gwiwar bankunansu da kuma nazarin alfanun faɗaɗa ayyukan bankunan Nijeriya a China.
Taron ya haɗa shugabannin kamfanoni, cibiyoyin kuɗi da sauran masu ruwa da tsaki da ke gudanar da harkokin kasuwanci a Nijeriya da China. Mahalarta sun yi musayar bayanai da gogewa, tare da duba hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin da ake fuskanta yayin aika kuɗi da gudanar da hada-hadar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ya jaddada muhimmancin tattaunawa kai tsaye da ’yan kasuwa domin fahimtar matsalolin kuɗi da na hukumomi da ke kawo cikas ga harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu. Ya ce, bayanan da kamfanonin da ke gudanar da ayyuka a ƙasashen biyu za su bayar za su taimaka wa babban bankin wajen gano wuraren da ake buƙatar ingantawa, domin sauƙaƙa hada-hadar kuɗi da bunƙasa zuba jari.
Wannan tattaunawa na zuwa ne a daidai lokacin da dangantakar kasuwanci tsakanin Nijeriya da China ke ƙara faɗaɗa, inda kamfanonin ƙasashen biyu ke gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban, ciki har da kasuwanci, masana’antu, bunƙasa ababen more rayuwa, fasaha da sauran harkokin tattalin arziki. A ’yan shekarun nan, cinikayya tsakanin Nijeriya da China ta ƙaru sosai, inda jimillar kuɗin cinikayyar ƙasashen biyu ta kusan kai dala biliyan 20.
Wani rahoto na baya-bayan nan ya kuma nuna cewa Nijeriya ta shigo da kayayyaki daga China da kuɗinsu ya kai naira tiriliyan 11.01 a rabin farko na shekarar 2026. Wannan adadi ya kai kusan kashi 40 cikin 100 na jimillar kayayyakin da Nijeriya ta shigo da su daga ƙasashen waje a lokacin.
Sai dai, gudanar da hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashe na iya jefa ’yan kasuwa cikin matsaloli da suka haɗa da jinkirin sarrafa kuɗaɗen biyan kaya, rashin ingantacciyar hulɗa tsakanin bankuna, wahalar samun kuɗin waje da kuma tsawon lokacin da ake ɗauka kafin kuɗin da aka tura ƙetare su isa inda aka nufa. Ga masu shigo da kaya, masu fitar da kayayyaki da masu zuba jari, jinkiri ko matsalolin biyan kuɗi na iya ƙara kuɗin gudanar da kasuwanci, kawo cikas ga ayyukan kamfanoni da kuma dagula shirye-shiryen tafiyar da kuɗaɗensu.
Saboda haka, Babban Bankin Nijeriya na ganin cewa inganta haɗin gwiwar bankuna zai taimaka wa ’yan kasuwa wajen gudanar da biyan kuɗi cikin sauƙi, tare da ƙarfafa dangantakar kasuwanci tsakanin tattalin arzikin ƙasashen biyu.
Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya mai kula da manufofin tattalin arziki, Philip Ikeazor, ya jaddada buƙatar mayar da ci gaban da aka samu a muhimman alamomin tattalin arzikin Nijeriya zuwa ƙarin zuba jari da kuma inganta kasuwannin kuɗi. Ya kuma bayyana muhimmancin tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa suna samar da damammaki na zahiri ga ’yan kasuwa da masu zuba jari, musamman ta hanyar inganta hanyoyin da ake bi wajen karkatar da jari zuwa ayyukan da za su bunƙasa tattalin arziki.
Jakadan Nijeriya a Chana, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya), shi ma ya yi jawabi ga mahalarta taron. Sauran waɗanda suka gabatar da jawabi sun haɗa da shugabar rukunin kamfanonin Blue Diamond Group, Festus Mbisiogu, da shugabar kamfanin CIG Motors, Cif Diana Chen. Sun bayyana ra’ayoyinsu bisa gogewar da suka samu wajen gudanar da kasuwanci tsakanin Nijeriya da China.
Babban Bankin Nijeriya ya ce, wani muhimmin ɓangare na taron shi ne zaman tattaunawa da sauraron ƙorafe-ƙorafe da shawarwarin mahalarta. Wannan ya ba ’yan kasuwa damar bayyana matsalolin da suke fuskanta wajen biyan kuɗi tsakanin ƙasashen biyu, tare da ba da shawarwarin inganta haɗin gwiwar harkokin kuɗi.
ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna shi ne yiwuwar faɗaɗa ayyukan bankunan Nijeriya a Chana. A cewar bankin, ƙara yawan bankunan Nijeriya da ke da ayyuka a China na iya sauƙaƙa wa kamfanonin Nijeriya samun hidimomin banki yayin gudanar da harkokinsu a kasuwar Asiya. Haka kuma, hakan zai taimaka wa kamfanonin China da ke son zuba jari ko faɗaɗa ayyukansu a Nijeriya.
Matakin zai iya ƙarfafa dangantaka tsakanin cibiyoyin kuɗi, tare da sauƙaƙa wa ’yan kasuwa kafa tsarin hulɗar banki da zai dace da buƙatun kasuwancinsu. Sai dai, cimma waɗannan manufofi zai buƙaci ci gaba da tattaunawa da bankuna da hukumomin da ke kula da harkokin kuɗi a ƙasashen biyu.
An kuma yi wa mahalarta bayani kan sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya, ingantuwar wasu muhimman alamomin tattalin arziki da kuma sabbin damammakin zuba jari da ke kunno kai a kasuwannin kuɗin ƙasar. An shirya taron ne domin bai wa masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwancin ƙasashen duniya cikakken haske kan alƙiblar tattalin arzikin Nijeriya da damammakin da ke akwai ga masu son zuba jari.
A jawabin rufe taron, Cardoso ya jaddada muhimmancin amfani da bayanai da shawarwarin ’yan kasuwa wajen gano matsalolin da ke buƙatar ɗaukar mataki a ƙarƙashin dokoki da nauyin gudanarwar Babban Bankin Nijeriya. Babban bankin ya ce bayanan da aka tattara daga taron za su taimaka wajen jagorantar tattaunawarsa da cibiyoyin kuɗi da hukumomin kula da harkokin kuɗi na ƙasashen biyu, tare da ba da fifiko ga wuraren da za a iya samun haɗin gwiwa mai amfani.
A cewar bankin, ana sa ran tattaunawar za ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin gwiwar tsarin kuɗi da magance matsalolin da ke addabar kamfanonin da ke gudanar da harkokin kasuwanci tsakanin Nijeriya da China.
Taron na Beijing na daga cikin manyan dabarun Babban Bankin Nijeriya na ƙarfafa dangantakar harkokin kuɗi ta Nijeriya da ƙasashen Asiya. Ya biyo bayan wasu tarurrukan tattaunawa da aka gudanar a ƙasar Singapore da kuma yayin taron shekara-shekara na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya, wanda aka gudanar a birnin Bangkok.
Ta hanyar waɗannan tattaunawa, Babban Bankin Nijeriya na ƙoƙarin ƙarfafa hanyoyin haɗin gwiwar kuɗi da ke tallafa wa kasuwanci, zuba jari da faɗaɗa ayyukan kamfanoni. Haka kuma, yana neman hanyoyin da za su sa biyan kuɗi tsakanin ƙasashen biyu ya fi sauƙi, sauri da inganci.
