Daga AISHA ASAS
Tauraruwar shirye-shiryen talabijin ta Najeriya, Natacha Akide, wadda aka fi sani da Tacha, ta buƙaci masu shirya shirin Big Brother Naija da su dakata na ɗan lokaci domin sake nazarin yadda suke gudanar da shi, tare da samar da sabbin dabarun da za su dawo da sha’awar masu kallo.
Tacha ta bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da ita a shirin Arise 360 na gidan talabijin na Arise News, inda ta yi nuni da cewa yanayin nishaɗi ya sauya sosai, musamman sakamakon yadda kafafen sada zumunta suka mamaye tattaunawar jama’a da kuma yadda suke samun labaran da ke jan hankalinsu.
A cewarta, lokacin da BBNaija ya fara samun karɓuwa sosai, kafafen sada zumunta ba su kai matsayin da suke a yau ba wajen jan hankalin jama’a. Amma yanzu, mutane na iya samun nishaɗi da tattaunawar da za su shafe sa’o’i suna bi a intanet, ba tare da sai sun jira wani shiri a talabijin ba.
Tacha ta yi amfani da rikicin iyali da ke tsakanin ’yan uwan mawaƙa, Peter da Paul Okoye, da aka fi sani da P-Sƙuare, a matsayin misali na yadda abubuwan da ke faruwa a kafafen sada zumunta za su iya mamaye hankalin jama’a, har ma a lokacin da ake gudanar da shirye-shiryen talabijin.
Saboda haka, ta yi imanin cewa masu shirya BBNaija na bukatar su sake tunanin yadda za su sa shirin ya bambanta da abin da masu kallo suka saba gani. Ta kuma ba da shawarar cewa dakatar da shirin na ɗan lokaci na iya sa jama’a su sake kewarsa, ta yadda dawowarsa za ta kasance da sabon salo da ƙarin abin da zai ja hankalinsu.
Tacha ta ce masu shirya shirin ya kamata su samar da sabbin dabaru masu kayatarwa, domin a cewarta, ’yan Najeriya sun saba da abubuwa da dama a duniyar nishaɗi, don haka yana da muhimmanci a kawo musu wani abu na daban.
Tauraruwar ta shahara ne a shekarar 2019, lokacin da ta shiga shirin BBNaija mai taken Pepper Dem. Sai dai an kore ta daga gidan bayan wani rikici da ya haɗa ta da abokiyar takararta, Mercy Eke.
Kiranta na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattauna makomar shirye-shiryen gasar talabijin irin BBNaija, musamman yadda za su ci gaba da jan hankalin masu kallo a lokacin da kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin nishaɗin intanet ke ƙara samun karɓuwa.
