Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamitin Yaƙin neman zaɓen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da ya yi bayani kan wasu saɓani da ya ce akwai a bayanan karatun Shugaba Bola Tinubu, bayan Tinubu ya soki karatun Atiku.
Saɓanin ya biyo bayan kalaman da Shettima ya yi a taron koli na tattalin arzikin Nijeriya karo na 32, wanda aka gudanar a Abuja ranar Litinin, inda ya soki shawarar Atiku na bayar da tallafin man fetur da aka tace a cikin gida, tare da tambayar ƙwarewarsa wajen tafiyar da tattalin arzikin Nijeriya.
Da yake magana kan horon da Atiku ya yi a Makarantar Koyon Aikin Lafiyar Muhalli ta Kano (Kano School of Hygiene), Shettima ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba shi da ƙwarewar da ake buƙata wajen tafiyar da tattalin arzikin zamani.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tambaya kan ilimin Atiku a fannin lafiyar jama’a, yana mai cewa zai iya samun matsala wajen bambance cutar mura da Ebola.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan rana, Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Dabarun Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Phrank Shaibu, ya zargi Shettima da yin ba’a ga matsayin karatun Atiku.
“Mece ce ainihin abin kunya game da karatun Atiku? Ya kammala sakandare, ya ci gaba da samun ƙarin horo, sannan ya gina rayuwarsa ta hanyar aiki,” in ji shi.
Shaibu ya tambayi dalilin da ya sa wata takarda da ake dangantawa da bayanan karatun Tinubu a Jami’ar Jihar Chicago (Chicago State Uniɓersity) ta nuna cewa ya halarci Goɓernment College Lagos a shekarar 1970, alhali rahotanni sun nuna cewa an kafa makarantar ne a shekarar 1974.
“Idan Shettima yana son bincikar bayanan karatun makaranta, ya kamata ya fara da mutumin da yake yi wa aiki,” inji shi.
Yaƙin neman zaɓen Atiku ya kuma yi nuni da sunan “Tinubu Bola Adekunle” da ke kan takardar shaidar yi wa ƙasa hidima ta NYSC da aka gabatar cikin takardun zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu, da kuma shari’o’in da aka taɓa yi kan tarihin karatunsa.
Batun Goɓernment College Lagos ya daɗe yana cikin muhawarar da ake yi a bainar jama’a. Sai dai, kasancewar wannan bayanin yana cikin takardar da ake takaddama a kanta, ba ya tabbatar da cewa Tinubu ya ƙirƙiri ko ya yi jabun takardun shaidar karatunsa.
Saɓani kan tallafin man fetur
Yaƙin neman zaɓen Atiku ya kuma yi watsi da sukar da Shettima ya yi wa shawarar Atiku ta bayar da tallafin man fetur da aka tace a Nijeriya.
Atiku ya gabatar da shawarar tsarin tallafi mai iyaka, wanda za a gudanar da bincike mai zaman kansa a kansa domin tabbatar da yadda ake kashe kuɗaɗen. Yaƙin neman zaɓensa ya ce wannan tsarin zai bambanta da tsohon tsarin tallafin man fetur.
“Idan Shettima yana ganin ba za a iya samun kuɗin aiwatar da shirin ba, to ya fito da alkaluman da ke nuna hakan, sannan ya gabatar da wata hanya mafi kyau ta rage farashin man fetur,” inji Shaibu.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da gaza rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin tsadar abinci, sufuri da man fetur.
