
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar Sakkwato, Hon. Manir Ɗan’iya ya tsallake rijiya da baya bayan wasu ‘yan bindiga sun buɗe wa ayarin motocinsa wuta a kusa da filin jiragen sama na Sultan Abubakar na III a daren wayewar Asabar.
Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar 30 ga Oktoba, 2026 jim-kaɗan bayan Ɗan’iya ya yi rakiya ga tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato kuma Sanatan Sakkwato ta Kudu, Aminci Waziri Tambuwal zuwa filin jirgin. An ga yadda motarsa mai gilasan kariyar harsasai ta samu dameji a wasu daga cikin gilasan nata.
Da take tabbatar da aukuwar lamarin, rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin Kakakinta DSP Ahmad Rufa’i, ta ce labari aukuwar lamarin a filin jiragen saman kuma za ta ɗauki matakan da suka dace a kai. Ta bayyana cewa, za a hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a ciki bisa yadda dokar ƙasa ta tanada.
Saidai, a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Abdullahi ya fitar, Ɗan’iya ya yi zargin cewa wasu jami’an Sokoto Marshal da Sokoto State Community Guard, sun tare ayarin motocin nasa tare da hana su wucewa ta yankin filin jiragen. A cewar sanarwar, jami’in da ya gana da su ya ce suna aiki ne bisa umarni daga manyansu kan cewa kada su bar mambobin ADC a Jihar Sakkwato su yi walwala.
Ta kuma yi zargin cewa yunƙurin jami’an tsaron da ke ba wa Ɗan’iya kariya na su kwantar da hankali yayin musayar kalaman bai yi nasara ba musamman ganin yadda aka riƙa harbe-harbe, inda a nan ne aka yi motoci masu kariyar alburusai dameji.
Sannan, sanarwar ta yi iƙirarin cewa an tsare wasu jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da aka tura aiki da ɗan takarar ADCn, tana mai kira ga a gaggauta sako jami’an.
Gwamnatin Jihar Sakataren ko hukumar tsaron al’ummar jihar ba su bayar da amsa ba ga waɗannan zarge-zarge an lokacin haɗa wannan rahoto.
