Sojoji sun ƙwato bindigu 52 a Borno da Yobe bayan halaka mayaƙa ISWAP 48

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sojojin Nijeriya sun yi nasarar halaka mayaƙan ƙungiyar ISWAP tare da ƙwato wasu makamai guda 52 yayin musayar wuta a jihohin Borno da Yobe.

Dakarun tsaro ƙarƙashin Atisayen Haɗin Kai na JTF da ke Arewa maso Gabas, sun daƙile wasu hare-hare a sansanonin sojoji da ke Bitta da Natt Buni Yadi a tsakanin 29 da 30 ga Oktoba, 2026. Jami’in yaɗa labarai rundunar na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni ne ya bayar da wannan labari a wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja.

A cewarsa, sojoji sun daƙile wani mummunan hari a sansaninsu da ke Bitta a daren ranar 29 ga Oktoba ta wani salon aiki da ya ƙunshi dakarun ƙasa da agajin na sama. Ya ce, dakarun sun kuma ƙaddamar da wasu hare-hare a wata babbar tawagar mayaƙan na ISWAP, waɗanda suke farmaki Natt Buni Yadi daga ranar 29 ga Oktoba har zuwa sa’o’in farko na ranar 30 ga watan.

Goni ya bayyana cewa, an ɗauki tsawon sa’o’i biyar ana fafatawa a tsakanin ɓangarorin biyu, wanda rundunar Theater Command ta sojin ta tsara tare da taimakon bayanan sirri, samun abin hari da kuma amfani da ƙarfin dakarun ƙasa da sama.

“Atisayen ya yi sanadiyyar halaka ‘yan ta’adda 48, yayin da sojoji suka ƙwato bindigar AK-47 guda 42, PKT machine gun biyar, bindiga mai sarrafa harsasai ta ƙasa guda huɗu da kuma tutur harbi mai girman 60mm,” inji shi. Sauran ababen da aka ƙwato sun haɗa da akwatin harsasan AK-47 105, kyamarorin bidiyo biyu da kuma tarin alburusai. Alburusan sun haɗa da guda 30 na 12.7mm, guda 2,738 na 7.62mm na musamman, 223 na 7.62mm na NATO da kuma 2,054 na PKT, kamar yadda ya bayyana a sanarwar.

Saidai, Kyaftin Goni ya ƙara da cewa soja guda ya rasa rayuwarsa yayin arangamar, inda kuma wasu biyu suka samu wasu ƙananan raunuka kuma ana musu magani, yana mai cewa rundunar ta duƙufa wajen bayar da kariya ga rayukan jami’anta da kuma hana walwala ga ‘yan ta’adda da ayyukansu a shiyyar da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply