Raba wa matasan APC motocin alfarma cin mutuncin talakawan Nijeriya ne – Atiku 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Atiku Abubakar, ya soki rahotannin da ke cewa an raba motocin alfarma na SUV ga shugabannin matasan jam’iyyar APC.

Atiku, wanda yake neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da fadar shugaban ƙasa su bayyana inda kuɗin sayen motocin suka fito.

Rahotanni sun nuna cewa motocin na shekarar 2026 ne, kuma kowacce tana da darajar sama da naira miliyan 150. An ce uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ce ta bayar da motocin.

Atiku ya ce ’yan Nijeriya suna da haƙƙin sanin ko an sayi motocin da kuɗin uwargidan shugaban ƙasa ne, gudummawar wasu mutane ko kuma kuɗin gwamnati.

Ya tambayi dalilin kashe makudan kuɗi wajen siyasa a lokacin da jama’a ke fama da rashin abinci, tsadar sufuri da sauran buƙatun yau da kullum.

Haka kuma, Atiku ya ce ya kamata gwamnati ta bayyana yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur, musamman ganin yadda talakawa ke ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki.

Ya kuma soki abin da ya bayyana a matsayin nuna almubazzaranci da jin daɗin rayuwa daga wasu mutanen da ke kusa da shugaban ƙasa. Ya ambaci rahotannin tafiyar shugaban matasan APC da jirgin sama mai zaman kansa, da kuma hotunan Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa, sanye da agogon hannu da aka ruwaito cewa darajarsa ta kai dala 500,000.

Atiku ya yi alƙawarin cewa idan ya zama shugaban ƙasa, za a binciki duk wani kuɗin gwamnati da aka kashe ba bisa ƙa’ida ba, kuma za a hukunta waɗanda aka samu da laifi.

“Tinubu ya sanya rayuwa ta yi wahala. Ni kuma zan sake sanya rayuwa ta zama mai sauƙin araha,” inji Atiku

By ukarofi

Leave a Reply