Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi gargaɗin cewa duk wani abokin ciniki da ya ƙi mayar da kuɗin da aka tura wa asusunsa bisa kuskure ga mai kuɗin, na iya fuskantar hukuncin ɗaurin gidan yari na tsakanin shekara biyar zuwa 10.
Gwamnan bankin, Olayemi Cardoso, ne ya yi wannan gargaɗi a ranar Alhamis, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a birnin Ibadan, Jihar Oyo. Ya buƙaci ’yan Nijeriya da su guji riƙe kuɗin da aka tura wa asusunsu bisa kuskure, tare da yin taka-tsantsan wajen bayyana bayanan asusun bankinsu ga ’yan damfara.
Cardoso, wanda ya gabatar da saƙonsa ta bakin kakakin bankin, Hakama Sidi Ali, ya ce samun bayanan asusun wani ta hanyar zamba da kuma ƙin mayar da kuɗin da aka tura wa asusu bisa kuskure laifuffuka ne da doka ta tanadar wa hukunci mai tsanani. Ya ce, “Abokin ciniki da ya ƙi mayar da kuɗin da aka tura wa asusunsa bisa kuskure ga mai kuɗin, na iya fuskantar hukuncin ɗaurin gidan yari na shekara biyar zuwa 10.”
An gudanar da taron ne a cibiyar taruka ta Jogor da ke Ibadan, ƙarƙashin taken: “Samar da Tsarin Kuɗi Mai ƙarfi, Inganci Komai Domin Bunƙasa Tattalin Arziki Mai ɗorewa.”
Taron wani ɓangare ne na shirin CBN Listens, wanda ke samar da dama ga bankin domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan manufofin harkokin kuɗi da kuma kare haƙƙin masu amfani da ayyukan banki. Cardoso ya ce an ƙirƙiri shirin ne domin bayyana manufofin bankin ga jama’a, gyara fahimtar da ba ta dace ba, da kuma tattara ra’ayoyi kan matsalolin da ke shafar mutane, ’yan kasuwa da al’ummomi. Ya sake jaddada ƙudurin CBN na tabbatar da daidaiton kuɗi da tsarin harkokin kuɗi, ƙarfafa amincewar jama’a da harkokin banki, da kuma faɗaɗa damar samun ayyukan kuɗi ga al’umma.
Gwamnan ya yi bayanin wasu muhimman sauye-sauyen da bankin ya aiwatar, ciki har da ƙaddamar da Lambar Tabbatar da Shaidar Abokin Ciniki ta Banki (BɓN) ga ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, sauye-sauyen tsarin hada-hadar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, shirin hangen nesa na tsarin biyan kuɗi na Nijeriya na shekarar 2028, da kuma ƙaddamar da sabon tsarin ƙididdigar kuɗin ruwa na hada-hadar kuɗi ta dare a Nijeriya.
A cewarsa, waɗannan matakai na da nufin inganta yadda ake tafiyar da yawan kuɗaɗen da ke yawo a tsarin banki, rage haɗurra, ƙarfafa ginshiƙan kasuwannin kuɗi da tallafa wa ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa. Cardoso ya bayyana cewa bai wa kowa damar amfani da ayyukan kuɗi na daga cikin muhimman manufofin bankin. Ya ce CBN na aiki tare da bankuna, kamfanonin fasahar kuɗi, masu gudanar da harkokin kuɗin hannu, abokan hulɗar ci gaba da gwamnatocin jihohi domin faɗaɗa ayyukan kuɗi zuwa yankunan da har yanzu ba su samu isasshen damar amfana da su ba.
Gwamnan ya kuma tunatar da abokan cinikin bankuna cewa suna da haƙƙin kai ƙorafinsu zuwa Sashen Kare Haƙƙin Masu Amfani da Ayyukan Kuɗi da Bunƙasa Shigar Jama’a CBN, idan bankunan da suke hulɗa da su suka kasa magance matsalolinsu. Ya ce kwastomomi za su iya kai ƙorafi ga CBN idan bankinsu ya gaza tabbatar da karɓar ƙorafin cikin kwanaki uku daga ranar da aka gabatar da shi, ko kuma ya kasa warware matsalar cikin wa’adin da dokokin kare haƙƙin masu amfani da ayyukan kuɗi suka tanada.
