Kotu ta bada umarnin maye Uzodinma da Okorocha a takarar sanata

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta umurci Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, da ya daina bayyana kansa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Imo ta Yamma a zaɓen da za a gudanar ranar 16 ga Janairu, 2027.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa, mai shari’a Obiora Egwuatu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, inda ya ce Uzodinma bai lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar 18 ga Mayu ba.

Alƙalin ya bayyana cewa hujjojin da aka gabatar a gaban kotun sun nuna cewa tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ne ya samu mafi yawan ƙuri’un da suka dace a zaɓen fidda gwani.

Saboda haka, kotun ta umarci APC da ta miƙa sunan Okorocha ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Imo ta Yamma a zaɓen 2027.

Haka kuma, kotun ta umarci INEC da ta wallafa sunan Okorocha a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen.

Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

By ukarofi

Leave a Reply