
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Ekiti da ke Kudu maso Yammacin Nijeriya, ta yi watsi da rahotannin da ke iƙirarin cewa wasu ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore a garin Ado-Ekiti, Baban Birnin jihar.Da fari, rahotanni sun bayyana cewa, ba a san takamaiman wajen da Sowore yake ba bayan zargin an sace shi.
Wani shaida ya ce al’amarin ya auku ne a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026, a wani sanannen wajen siyar da abinci da ke babban birnin jihar, inda aka ce wasu ‘yan bindiga sun afka tare da yin garkuwa da ɗan gwagwarmayar. Shaidan ya bayyana maharan a matsayin ‘yan barnadar siyasa da ake zargin suna da alaƙa da jam’iyya mai mulki APC.
Saidai, yayin tsokaci kan wannan batu, rundunar ‘yan sandan jihar ta ƙaryata zargin garkuwar, inda ta bayyana hakan a matsayin zance maras asali da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a. A sanarwar da kakakin rundunar, SP Sunday Abutu ya fitar, ta ce an yi cacar baki a tsakanin Sowore da wasu mutane a wani wajen cin abinci da ke yankin Dalimore a Ado-Ekiti, wanda bayan haka ne aka hanzarta sanar da ‘yan sanda.
Rundunar ta ce, batun cewa an yi garkuwa da Sowore ba gaskiya ba ne domin jami’anta sun je wajen kuma sun ceto shi. Saidai, ta ce ya samu wasu ƙananan raunuka yayin musayar kalaman kuma yana asibitin ‘yan sanda a Ado-Ekiti yana karɓar magani.
Akan haka ne Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Falade Adegoroye Michael ya umarci a gudanar da bincike kan al’amarin tare da kama dukkan wanda aka samu da hannu a ciki domin gurfanarwa a gaban doka. Haka kuma, rundunar ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankali tare da ƙaurace wa labarai marasa tushe da kuma kauce wa yaɗa su.

