Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai saɓani tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, yana mai jaddada cewa babu wata matsala ta ƙashin kai tsakaninsa da tsohon gwamnan.
Sani ya ce, bai taɓa yin magana a kan El-Rufai ta hanyar suka ko cin mutunci ba, kuma har yanzu yana da niyyar ci gaba da kyakkyawar mu’amala da shi, duk da raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan bambance-bambancen siyasa tsakaninsu. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Trust Tɓ, inda ya yi tsokaci kan rahotannin da ke nuna cewa dangantakarsu ta lalace. “Ba ni da wata matsala da El-Rufai; ban taɓa yin magana a kansa ta hanyar suka ba,” inji Sani.
Ya zargi wasu masu neman cin moriyar siyasa da ƙara gishiri a kan zargin saɓanin, domin haifar da tashin hankali ba tare da wani dalili ba da kuma rura rikicin siyasa a Jihar Kaduna. A cewarsa, raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan dangantakarsa da tsohon gwamnan ba su nuna ainihin abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba ba, domin gwamnatinsa ta mayar da hankali ne kan gudanar da mulki da samar wa al’umma romon dimokuraɗiyya.
Gwamnan ya nuna damuwa kan yadda wasu mutane ke amfani da rahotannin saɓani tsakaninsa da El-Rufai wajen haddasa rarrabuwar kai a jihar. Ya jaddada cewa irin wannan hasashe ba shi da amfani, kuma yana iya karkatar da hankalin gwamnati daga nauyin da ke kanta na magance matsalolin al’umma. Sani ya buƙaci al’ummar Jihar Kaduna da su yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa yana fafatawa da tsohon gwamnan a fagen siyasa.
Haka kuma, ya bayyana cewa ba shi da niyyar shiga yaƙin neman rinjaye ta kafafen yaɗa labarai, yana mai cewa babban abin da ya sa a gaba shi ne haɓaka haɗin kai tsakanin al’ummomin jihar masu bambancin ra’ayoyi da al’adu, tare da ci gaba da ayyukan raya ƙasa. Gwamnan ya sake tabbatar da girmamawarsa ga El-Rufai, yana mai bayyana shi a matsayin wanda ya gabace shi a kujerar gwamna, kuma shugaba wanda har yanzu yake girmama matsayinsa.
Sani ya dage cewa bai kamata a ɗauki raɗe-raɗin siyasa a matsayin hujjar cewa akwai saɓani na kashin kai tsakaninsa da tsohon gwamnan ba. Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mai da hankali kan gudanar da mulki, maimakon barin tattaunawar jama’a kan dangantakarsa da El-Rufai ta mamaye ayyukan da ya kamata ta gudanar.
Wannan furuci na gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rade-radin dangantakar siyasa tsakaninsa da El-Rufai, tun bayan da ya gaji tsohon gwamnan a shekarar 2023. Dukansu mambobi ne na jam’iyyar APC, duk da cewa dangantakar siyasa tsakaninsu ta ci gaba da jan hankalin jama’a a Jihar Kaduna.
Sani, wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2023, ya sha jaddada muhimmancin haɗin kai da shugabanci da ya haɗa kowa da kowa a jihar. Ya ce har yanzu babban burinsa shi ne haɗa kan al’umma, ƙarfafa ayyukan ci gaba da kuma tabbatar da cewa mazauna jihar sun amfana da manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
Gwamnan ya buƙaci ’yan siyasa da sauran mazauna jihar da su guji yaɗa zarge-zargen da ba a tabbatar da sahihancinsu ba game da dangantakarsa da El-Rufai, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta bari irin waɗannan raɗe-raɗi su kawar da ita daga gudanar da ayyukanta ba.
