PDP za ta kawo ƙarshen zaman banza da rashin aiki a tsakanin matasa a Nasarawa 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a ƙaramar Hukumar Nasarawa, ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Hon. Jamilu Muhammad Ahmad, ya bayyana bikin al’adar al’ummar Marghi mazauna Jihar Kano a matsayin abin sha’awa da kuma babbar nasara ga al’ummar.

Hon. Jamilu ya bayyana hakan ne bayan halartar bikin al’adar Yawal da kuma bikin cika shekara ɗaya da naɗa Sarkin Marghi na Kano, “Ptil Margi”, Wadzani Adamu Mamza, a kan karagar mulki.

Ya ce abin a yaba ne yadda al’ummar Marghi ke riƙe da al’adunsu. Ya ƙara da cewa, idan aka yi la’akari da Jihar Kano baki ɗaya, ƙaramar Hukumar Nasarawa ce ke da kusan kashi 75 cikin 100 na al’ummomin ƙabilu daban-daban da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar, kuma ana ba su matsayinsu da darajarsu a matsayin ’yan’uwa.

Ya ƙara da cewa, “Nasarawa tamkar ƙaramar Nijeriya ce. Duk lokacin da ka zo za ka yi mulki, sai ka bai wa kowa ’yancinsa na ɗan ƙasa,” in ji shi.

Da yake magana kan matsalolin yankin, Hon. Jamilu ya ce babbar matsalar da suke fuskanta a yanzu a ƙaramar Hukumar Nasarawa ita ce rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Ya bayyana cewa, a matsayinsa na matashi kuma ɗan takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, sun lura da wannan matsala. Ya ce Allah ya azurta yankin da wuraren da za a iya samar wa matasa ayyukan yi, amma ’yan siyasa ba sa tunanin samar musu da irin waɗannan damammaki.

Ya ƙara da cewa idan Allah ya ba su dama, za su yi ƙoƙarin kawo ƙarshen zaman banza da rashin aikin yi a tsakanin matasa. Ya kuma ce za su yi kasafin kuɗi bisa tsarin zamantakewar al’umma, la’akari da yadda ƙaramar Hukumar Nasarawa ta ƙunshi ƙabilu daban-daban.

Saboda haka, ya yi kira ga al’ummar Nasarawa da su ci gaba da zaman lafiya da juna, kamar yadda aka san su da zaman lafiya da mutunta juna.

Hon. Jamilu Muhammad Ahmad ya bayyana goyon baya da haɗin kan da al’ummar ƙaramar Hukumar Nasarawa ke bai wa takararsa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a matsayin abin a yaba. Ya kuma buƙace su da su ci gaba da bai wa jam’iyyar ƙuri’unsu a zaɓe mai zuwa.

Ya ce a halin yanzu, babu inda jam’iyyar PDP ta fi ƙarfi da tasiri kamar a ƙaramar Hukumar Nasarawa, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Matasan Jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ibrahim Bala Aboki, da Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Alhaji Rabiu Wangal.

By ukarofi

Leave a Reply