
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ƙoƙarinta na rage tasirin tsadar rayuwa akan al’ummar ƙasa, Gwamnatin Tarayya ta ce ta fara aiwatar da shirin raba Naira 50,000 ga talakawa magidanta a sassan faɗin Nijeriya.
Ministan Jinƙai da Rage Talauci, Bernard Doro ne ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a Abuja, ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026, inda ya bayyana shirin fadar shugaban ƙasar a matsayin abin da aka shirya domin samar da tallafi ga miliyoyin talakawan ƙasar. Ya ce, an kafa shirin ne a ƙarƙashin Tsarin Samar da Tallafin Gaggawa da Ɗorewa na Ƙasa (NERSI) ganin yadda ake samun hauhawar farashin kayayyakin abinci da wasu kayayyakin amfanin yau da kulluma a matakin duniya, waɗanda ke cigaba da matsa wa zamantakewar al’umma.
A ƙarƙashin shirin, za a riƙa bai wa mutanen da suka cancanta N50,000 a kowane wata da nufin rage musu raɗaɗin matsin tattalin arziƙi, kamar yadda ya bayyana. Sannan, za a riƙa sabunta shirin akai-akai bisa la’akari da sauye-sauyen halin tsadar rayuwa, kuma za a riƙa sanar da masu amfana gabanin aiwatar da wani gyara a kai.
Kazalika, ya ce ma’aikatar tana aiki tare da abokan hulɗar kuɗi na dijital domin tabbatar da samun aiwatar da shirin akan lokaci bisa gaskiya da adalci yayin isar wa masu amfana. A cewarsa, za a tura wa magidanta saƙonnin kar-ta-kwana (SMS) domin neman amincewarsu gabanin biya kai tsaye ta asusun bankunansu.
Ya bayyana cewa, ba a buƙatar mutane su cike wata takarda da sunan son a saka su a tsarin, biyan wani kuɗi ko rajista ta hannun wasu wakilai domin shiga shirin. Ya gargaɗi al’umma akan ‘yan damara, yana mai shawartarsu da kada su bayar da bayanansu na ƙashin kai kamar su lambobin sirri (PINs) ko lambobin tantancewar banki (BVNs) ga kowaye. “Idan ka na kokwanton wani saƙo ko wani kira da wani da ya buƙaci ka biya wani kuɗi, ka kira layin neman agaji na NERSI ta 0700-022-2222,” inji shi.
