Kuɗin shigar ’yan Nijeriya ba ya iya ciyar da iyalansu – Minista

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin Nijeriya, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa wasu iyalai a ƙasar na kashe kuɗin da ya zarce abin da suke samu wajen sayen abinci, har ma wasu sukan ci bashi ko neman taimakon ’yan uwa domin su iya ciyar da iyalansu.

Oyedele ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a cibiyar nazarin harkokin ƙasa da ƙasa ta Chatham House da ke Landan. Ya ce wani binciken da gwamnati ta gudanar ya nuna cewa wasu iyalai na kashe kuɗin da ya kai kashi 120 cikin 100 na kuɗin shigarsu wajen sayen abinci.

A cewarsa, wannan yana nuna cewa samun aikin yi kaɗai bai wadatar wajen fitar da mutum daga talauci ba. Ya bayyana cewa duk da cewa yawan marasa aikin yi a Nijeriya ya kai kusan kashi biyar cikin 100, sama da rabin al’ummar ƙasar na rayuwa cikin talauci.

Ministan ya ce akwai mutane da ke da aikin yi, amma har yanzu ba sa iya biyan buƙatunsu na yau da kullum, musamman wajen samar da abinci. Ya jaddada cewa matsalolin tattalin arziki ba za su warware yadda ya kamata ba matuƙar jama’a ba su fara samun sauƙin rayuwa ba.

Oyedele ya bayyana cewa hauhawar farashin abinci na ci gaba da zama babban ƙalubale, duk da raguwar hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya. Ya ce hauhawar farashin abinci ya kai kashi 19.6 cikin 100 a watan Satumba, yayin da farashin wasu muhimman kayan abinci, kamar tumatir, garri da wake, bai ragu kamar na sauran kayayyaki ba.

Ya danganta tsadar abinci da ƙarancin amfanin gona, dogaro da noman kaka, rashin isassun wuraren ajiya, matsalolin sufuri da jigilar kayayyaki, da kuma rashin tsaro a wasu yankunan noma.

Ministan ya ce ana iya rasa har kashi 60 cikin 100 na tumatir bayan girbi saboda matsalolin adanawa da jigilar amfanin gona. Ya bayyana cewa irin wannan asara na rage yawan kayan abincin da ke isa kasuwanni, lamarin da ke ƙara tsadar da masu saye ke fuskanta.

Ya ce gwamnati na ƙoƙarin shawo kan matsalar ta hanyar zuba jari a fasahar noma, bunƙasa ban-ruwa domin manoma su riƙa noma a duk tsawon shekara, gina wuraren ajiya, inganta hanyoyin sufuri a yankunan karkara da kuma ƙarfafa tsaro a wuraren noma.

Oyedele ya ƙara da cewa gwamnati na faɗaɗa damar samun rance ga ƙananan manoma da ’yan kasuwa domin ƙara yawan amfanin gona da bunƙasa harkokin da ke samar da guraben ayyukan yi.

Dangane da tallafa wa iyalan da ke fama da matsin tattalin arziki, ministan ya ce shirin gwamnati na bayar da tallafin kuɗi kai tsaye ya kai ga gidaje sama da miliyan 10.

A cewarsa, ana biyan tallafin ta hanyar na’ura, tare da tantance waɗanda za su amfana ta amfani da lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN, domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga waɗanda aka tsara za su amfana da shi.

Ya ce gwamnati na kuma mai da hankali wajen bunƙasa noma da sauran harkokin kasuwanci da hidimomi domin ƙara kuɗin shiga da inganta rayuwar jama’a.

Sai dai ministan ya amince cewa har yanzu tsadar abinci na ci gaba da jefa iyalai da dama cikin mawuyacin hali.

Jawabin nasa ya nuna cewa, duk da wasu sauye-sauye da ake samu a wasu alamu na tattalin arzikin Nijeriya, iyalai da dama na ci gaba da fuskantar ƙalubalen biyan kuɗin abinci da sauran buƙatun yau da kullum.

By ukarofi

Leave a Reply