Gwamna Lawal ya miƙa sandar mulki ga Sarkin Gusau na 16

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Asabar ya miƙa sandar mulki ga Sarkin Gusau na 16, Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello na II.

Sarkin Gusau na daga cikin sarakuna masu daraja ta farko guda 19 da suka karɓi sandar mulki daga hannun Gwamnan a wani biki mai ƙayatarwa da aka gudanar a harabar baje kolin kasuwanci (Trade Fair Complex) da ke Gusau.

Masarautar Gusau, wacce ta samo asali tun daga Jihadin Shehu Usman Danfodiyo na ƙarni na 19, ita ce zuciya da kuma hedikwatar Jihar Zamfara a Arewa Maso Yammacin Najeriya. Malam Sambo Dan Ashafa, ɗaya daga cikin amintattu kuma wanda ya karɓi tuta daga Daular Sokoto ne ya kafa ta.

An naɗa Mai Martaba Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello na II a matsayin Sarkin Gusau na 16 a watan Yulin 2025, bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga Yuli, 2025, yana da shekaru 71 a duniya. Sabon Sarkin jikan gida ne kai tsaye ga wanda ya kafa masarautar.

A matsayin wani ɓangare na ayyukan bikin naɗin, majalisar masarautar Gusau ta shirya lacca ta musamman kan tarihi da rayuwar wanda ya kafa masarautar, Malam Sambo Dan Ashafa, wacce fitattun Malamai suka gabatar.

Bikin naɗin ya kuma haɗa da gagarumin bikin naɗin na sarautu, inda aka ba da manyan sarautun gargajiya ga manyan mutane da suka bayar da gagarumar gudummawa wajen ci gaban masarautar Gusau da Jihar Zamfara.

Da yake miƙa sandar mulki, Gwamna Lawal ya buƙaci sarakunan gargajiya na jihar da su taimaka wa gwamnati a kowane mataki wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa.

Gwamnan ya bayyana Sarkin Katsinan Gusau a matsayin shugaba mai tawali’u, tausayi, ladabi da kuma kishin jama’a, yana mai nuna ƙwarin gwiwar cewa zamanin mulkinsa zai kawo zaman lafiya da ci gaba.

“Ana sa ran shugabannin gargajiya su zama masu kula da jama’arsu da kuma al’adunsu. Ina kira gare ku da ku zama abin koyi na haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba, tare da inganta zaman lafiya a tsakanin jama’arku da ma faɗin Jihar Zamfara da ƙasa baki ɗaya,” in ji Gwamna Lawal.

Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Sarkin Gusau na 16 zai samar da shugabanci na ƙwarai wanda zai inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewar Masarautar, Jihar Zamfara da Najeriya baki ɗaya.

A nasa jawabin, Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello na II, ya gode wa Gwamna Dauda Lawal bisa wannan karamci tare da alƙawarin samar da shugabanci na kowa da kowa wanda zai inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.

Sarkin ya tabbatar da cewa zai tsaya tare da dukkan jama’arsa, ya tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban nasarautar, tare da kira ga al’ummar Gusau da Jihar Zamfara da su ci gaba da zama masu bin doka da oda da kuma mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya wajen dawo da zaman lafiya.

Taron mai ƙayatarwa ya samu halartar mambobin majalisar zartarwa ta Jihar Zamfara, ‘yan majalisar dokoki ta jiha da ta ƙasa, tsofaffin Gwamnoni, Sarakuna daga ciki da wajen jihar, manyan ‘yan kasuwa, shugabannin addini da dubban jama’a masu nuna ƙauna da suka yi cincirindo zuwa Gusau domin shaida wannan gagarumin tarihi.

By ukarofi

Leave a Reply