INEC ta fara tantance ‘yan jarida don zaɓukan 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta ce ta fara aikin tantancewa ta intanet ga ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai da ke sa ran za su yi aikin yaɗa rahotannin zaɓukan 2027.

An tsara zaɓukan Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Dokokin Ƙasa ne a ranar 16 ga Junairu, 2027, yayin da za a gudanar da na gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

INEC, a wani saƙo da ta wallafa a ranar Juma’a, ta shawarci gidajen jarida da ke da ra’ayin ɗauka da yaɗa rahotannin da su ziyarci adireshi kamar haka: https://imap.inecnigeria.org”>https://imap.inecnigeria.org domin yin rajista.

A cewarta, shafin, wanda aka buɗe a ranar 30 ga Oktoba, za a rufe shi ne a ranar 1 ga Disamba, 2026. Hukumar ta yi gargaɗin cewa ba za ta karɓi rajistar waɗanda suka yi jinkiri ba domin shafin zai rufe kansa ne kai-tsaye da zarar wa’adin da aka bayar ya cika.

INEC ta kuma shawarci masu ra’ayin rajista su kira lambobi kamar haka domin neman ƙarin bayani 08063041332 ko 08032861058, ko aike mata da saƙon imel ta adireshi: [email protected], kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ya bayyana.

By Babaji

Leave a Reply