Daga SANI GAZAS CHINADE a Damaturu
Sojojin Operation Haɗin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 48 a lokacin rikice-rikice daban-daban a yankunan Bita da Buni Yadi da ke jihohin Borno da Yobe, inda suka ƙwato makamai da dama da dubban harsasai.
Kaftin Mohammed Goni, muƙaddashin jami’in yaɗa labarai na Operation Hadin Kai, ya bayyana ayyukan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026.
Sojojin sun ce sun daƙile hare-hare a yankin Bitta, a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno da kuma makarantar horas da sojoji ta Arewa maso Gabas (NETTS) da ke Buni Yadi, a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Kamar yadda rahoton ke nunawa rikicin farko ya faru ne a daren ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, lokacin da sojoji da tallafin jiragen sama suka daƙile yunƙurin kai hari a yankin Bitta.
A Buni Yadi cikin jihar Yobe, sojoji sun ƙaddamar da farmakin ramuwar gayya bayan mayakan ISWAP sun kai hari kan wurin horas da sojoji a makare ranar Alhamis.
Sojojin sun ce faɗan ya ɗauki tsawon sa’o’i biyar, inda ya shafi sojojin ƙasa, jiragen sama, bayan an samu sa ido sakamakon samun bayanan sirri.
A cewar sanarwar, wannan aiki da dakarun sojan suka aiwatar an samu nasara akan ‘yan ta’adda 48 da aka hallaka, yayin da sojoji suka ƙwato tarin makamai da harsasai.
Makaman da aka ƙwato sun hada da bindigogin AK-47 guda 42, bindigogin harba harsasai na PKT guda biyar, bindigogin harba harsasai na gaba ɗaya guda huɗu da kuma makamin harba bama-bamai nau’in 60mm guda ɗaya.
Sojojin sun kuma ƙwato akwatunan harsasan AK-47 guda 105, kyamarorin bidiyo guda biyu da dubban harsasai na nau’o’i daban-daban.
Harsasan sun haɗa da guda 2,738 masu nauyin 7.62mm na musamman, guda 2,054 na harsasan PKT da kuma harsasan 7.62mm na NATO guda 223.
Sojojin sun kuma bayar da rahoton ƙwato harsasai masu huda sulke na 12.7mm.
Soja ɗaya ya mutu a lokacin rikicin, yayin da wasu biyu suka samu raunuka marasa tsanani kuma suna karɓar kulawar likitoci, a cewar sanarwar.
