Imam Rasheed ya zama magajin Marigayi Sheikh Yahaya Masussuka

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Al’ummar Musulmi da Kiristoci, tare da manyan malaman addini, masana da jami’an gwamnati na ciki da wajen Nijeriya, sun halarci wani gagarumin taron haɗin kai da ƙarfafa zaman lafiya da aka gudanar a filin wasa na Muhammadu Dikko .

An gudanar da taron ne ƙarƙashin ƙungiyar Unity Assembly for Peace (UAP), a matsayin wani ɓangare na bikin kammala tafsirin Alƙur’ani da Alƙur’ani (Tafsirul Qur’an Bil Qur’an wanda babban Malami Marigayi Sheikh Yahaya Masussuka ya kammala ‘yan satittka kafin ‘yan ta’adda su harbe shi a gidansa da ke Dutsin-ma da abokinsa tare da ci gaba da manufar marigayin ta gina al’umma mai haɗin kai, fahimtar juna da zaman lafiya.

Taron ya samu halartar manyan malaman addinai daga ɓangarorin Musulmi daban-daban, da suka haɗa da mabiya ɗariku, Ahlus-Sunnah, Shi’a da Qur’aniyyun, baya ga wakilan addinin Kiristanci. Haɗuwar, ta nuna muhimmancin tattaunawa da mutunta juna wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Daga cikin manyan baƙi da suka halarci taron akwai tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Barista Solomon Dalung, wanda ya gabatar da jawabi kan muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Haka kuma, taron ya samu halartar wakilin Sheikh Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky, Farfesa Abdullahi Danladi, wanda ya wakilci jagoran harkar musulunci a Nijeriya a wannan muhimmin taro.

Manyan malaman addinin Musulunci da suka gabatar da jawabai a wajan kuwa sun haɗa da Sheikh Muhammad Nuru, Sheikh Ibrahim Makwarari, babban malamin ɗarikar Ƙadiriyya, da Sheikh Yakubu Yahaya Katsina, Farfesa Abdullahi Danladi da sauransu.

A jawabansu, malaman sun jaddada muhimmancin koyarwar addini wajen gina kyakkyawar al’umma, haɗin kai, tare da kira ga jama’a da su ƙarfafa zaman lafiya, fahimtar juna da mutunta bambance-bambancen addinai a zamantakewarsu musamman a kasa irin Nijeriya mai yawan ƙabilu, aƙidoji da addinai.

Mahalarta taron sun kuma samu damar sauraron jawabai daga sauran manyan baƙi, waɗanda suka yi tsokaci kan buƙatar kauce wa rikice-rikice, ƙarfafa zumunci da kuma tabbatar da zaman tare tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Taron ya kasance wata dama ta musamman ta tunawa da gudummawar Marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, wajen amfani da koyarwar addini a matsayin wata hanya ta haɗa kan al’umma, gina zumunci da bunƙasa zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci.

Wani muhimmin al’amari da ya ɗauki hankalin mahalarta taron shi ne naɗin Imam Rasheed a matsayin magajin marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, wanda ya assasa wannan yunƙuri na haɗa kan al’umma da samar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristanci kafin ‘yan ta’adda su harbe shi a makon jiya a kofar gidansa.

Naɗin Imam Rasheed a matsayin magajin marigayin na daga cikin matakan da aka ɗauka domin tabbatar da ci gaba da wannan kyakkyawar manufa da marigayin ya assasa, abin da aka bayyanar da cewar, ta yadda ƙoƙarin da ya fara ba zai tsaya sakamakon kashe shi da ‘yan ta’addan suka yi ba.

Taron ya sake aika saƙo mai ƙarfi cewar “zaman lafiya ba nauyin gwamnati ko shugabannin addini kaɗai ba ne, alhakin dukkan al’umma ne. Haɗin kai, fahimtar juna da mutunta addinin juna, su ne ginshiƙan zaman tare da ci gaban kowace al’umma.”

Mahalarta taron sun yi addu’o’in Allah Ya jiƙan marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, ya dau fansar ‘yan ta’addan da suka yi masa wannan aika-aika, ya kuma saka masa da alheri bisa gudummawar da ya bayar, tare da neman Allah ya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Katsina, Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply