
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cibiyar Kula da Bayar da Kariya ga Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta ce ta samu rahotannin wasu marasa lafiya biyu da ake zargin suna ɗauke da cutar Ebola a Shiyyar Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda tuni aka killace su tare da ƙaddamar da bincike kan al’amarin.
Hukumar ta bayyana haka ne a sahihin shafinta na X a ranar Asabar, inda ta ƙara da cewa tana aikin gano haƙiƙanin al’amarin ta hanyar gwaje-gwaje da wasu ayyukan da suka shafi bincike cutar Ebola. A cewar NCDC, wannan al’amari dai zargi ne yayin da za a tabbatar bisa la’akari da sakamakon bincike.
Ta ƙara da cewa, kasancewar an ga alamun cutar a tare da su ba shi ke nuna sun kamu da ita ba har sai gwaji ya tabbatar da haka.
Akan haka ne NCDC shawarci al’umma da su cigaba da kasancewa masu kiyaye shawarwarin likitoci kan samun kariya daga kamuwa da cutar hanyar yawan wanke hannu akai-akai, zama cikin tsaftace da makamantansu. A ƙarshe, ta ce za a fitar da ƙarin bayani da zarar an samu wani ci-gaba kan al’amarin.
