MOPPAN ta yi jimamin rasuwar Barista Aminu Mai-Gaskiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa (MOPPAN) ta bayyana kaɗuwarta bisa rasuwar tsohon Mashawarcinta kan harkar shari’a kuma tsohon Sakatarenta na Jihar Sakkwato, Barista Aminu Abdullahi Maigaskiya.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026 mai ɗauke da sanya hannun Shugabanta, Shehu Hassan Kano, MOPPAN ta bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga iyalansa, MOPPAN reshen Sakkwato, Masana’antar Finafinan Kannywood da ɗaukacin masu harkar fim a Nijeriya.

A cewarta, yayin hidimarsa ga ƙungiyar, marigayin ya nuna ƙoƙari, jajircewa, ƙwarewa da sadaukarwa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa, tana mai cewa za a cigaba da tuna wannan gudummawa da ya bai wa MOPPAN musamman a jihar Sakkwato.

Don haka a madadin majalisar zartarwar MOPPAN ta ƙasa da mambobinta, shugaban ƙungiyar ya sanar da miƙa ta’aziyyarsu ga iyalai da dangin marigayin, MOPPAN reshen Sakkwato, Masana’antar Kannywood da sauran abokan hulɗa a faɗin Nijeriya da abokan arziƙi da dai sauransu.

Ta kuma yi masa addu’ar Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa kurakuransa tare da sanya shi a Aljannar Firdausi gami da bai wa makusantansa haƙurin juriyan rashin sa.

By Babaji

Leave a Reply