HION ta horar da AHOUN kan dabarun jigilar alhazai

Spread the love

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano

Cibiyar Horar da Dabarun Aikin Hajji ta Nijeriya (HION), ƙarƙashin jagorancin Farfesa Muhammad Nasiru Mai Turare, ta shirya wa ƙungiyar Kamfanonin Jigilar Alhazai zuwa Hajji da Umara ta Nijeriya (AHOUN) horo kan dabarun tunkarar ƙalubalen da ka iya tasowa sakamakon shirin mayar da aikin jigilar alhazai hannun kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaban cibiyar, Farfesa Muhammad Nasiru Mai Turare, ya bayyana hakan ne a wajen buɗe taron bitar na kwanaki uku da aka gudanar a Kano a farkon makon da ya gabata.

Ya ce tsarin da Saudiyya ke shirin aiwatarwa nan da shekarar 2030, wanda zai bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar gudanar da aikin jigilar alhazai, ya sa ya zama dole a horar da masu wannan aiki kan dabarun zamani domin su gudanar da shi cikin nasara.

Farfesa Mai Turare ya ce, sakamakon tattaunawa da fahimtar juna tsakanin hukumomin Saudiyya da na Nijeriya, za a fara bai wa kamfanonin jigilar alhazai masu zaman kansu kashi 30 cikin 100 na aikin, sannan a riƙa ƙara musu kaso a hankali har zuwa kashi 90 cikin 100, kafin a kai ga matakin da Saudiyya ta tsara.

A nasa jawabin, shugaban AHOUN, Malam Haruna Isma’ila, ya ce ƙungiyar ta daɗe tana neman irin wannan dama, yana mai cewa tsarin na iya taimakawa wajen rage matsalolin gudanar da aikin Hajji a kowace shekara, tare da inganta ayyukan da kuma rage farashi.

Ya ce kamfanonin sun daɗe suna gudanar da aikin jigilar masu zuwa Umara, inda ya bayyana cewa yawan masu zuwa Umara ya fi na masu zuwa Hajji. Ya kuma nuna kyakkyawan fata cewa ’yan ƙungiyar za su iya gudanar da aikin cikin nasara da taimakon Allah.

Malam Haruna ya yi kira ga Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) da ta taimaka wa kamfanonin ta hanyar samar musu da abubuwan da suke buƙata domin gudanar da aikin yadda ya kamata.

Ya kuma buƙaci Gwamnatin Nijeriya ta dawo da tsarin tallafin da ake bai wa masu tafiya ƙasashen waje, ciki har da alawus ɗin BTA da sauran matakai da dokoki da za su taimaka wa alhazai da kamfanonin da za su gudanar da aikin.

Shi ma Manajan Daraktan kamfanin Hamshy T.A, Mustapha Hamisu, ya bayyana aikin jigilar alhazai zuwa Hajji da Umara a matsayin mai daraja, yana mai cewa zai iya samar da ayyukan yi ga matasa.

Ya ce kamfaninsa na maraba da sabon tsarin da kuma horon da HION ta shirya, inda ya buƙaci a faɗaɗa irin wannan horo domin ya shafi sauran masu ruwa da tsaki a harkar, manya da ƙanana, saboda amfanin da za a samu.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban ƙasa na AHOUN, Alhaji Abdulaziz Sabitu Muhammad Arafat, ya bayyana ra’ayinsa cewa gudanar da aikin ta hannun kamfanoni na iya samar da sauƙi fiye da yadda ake gudanar da shi ta hannun hukumar.

Ya ce dangantaka tsakanin hukumomin Saudiyya da Nijeriya na iya bai wa ƙasashen damar sassautawa juna a wasu fannoni, amma irin wannan sassauci ba lallai ya kasance ga kamfanoni masu zaman kansu ba.

Ya kuma bayyana cewa tsarin kamfanoni na iya rage tsawon lokacin da alhazai za su yi a Saudiyya, inda ya kwatanta hakan da tsarin da NAHCON ke bi, wanda a cewarsa, alhazai kan shafe kwanaki 40 ko fiye.

A cewarsa, tsarin na iya bai wa masu ƙaramin ƙarfi damar shiga aikin gwargwadon kuɗaɗensu da ƙarfin kamfanoninsu.

By ukarofi

Leave a Reply