Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban ƙungiyar Sakataren Ilimi na ƙananan Hukumomi 44 na Jihar Kano, kuma Sakataren Ilimi na ƙaramar Hukumar Birni, KMC, Comrade Nura Sulaiman, tare da takwarorinsa na ƙananan hukumomin Wudil da Dala, sun yabawa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kan ƙoƙarin bunƙasa ilimi tun daga matakin farko har zuwa manyan makarantu.
Da yake magana, Comrade Nura Sulaiman ya ce shugaban ƙaramar Hukumar Birni, Hon. Saleem Hashim, ya tsaya tsayin daka wajen inganta harkokin koyo da koyarwa a ƙaramar hukumar, ta hanyar gyaran makarantu da gine-gine a dukkan mazabun da suke ƙarƙashinta.
Ya ce shugaban ƙaramar hukumar yana sa ido kan ayyukan malamai, kuma a kai a kai yana ziyartar makarantu domin tabbatar da cewa kowa yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
Nura Sulaiman ya ce wannan misali ne na kyakkyawan shugabanci irin wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke nunawa. Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar kan amincewa da ɗaga darajar ma’aikatan koyarwa 18,000 a lokaci guda, tare da sauran shirye-shiryen tallafa wa ilimi, gina makarantu da tura ɗalibai karatu a ƙasashen waje.
Ya ƙara da cewa Kano ta yi fice wajen samun nasara a jarrabawar NECO har sau biyu, yana mai danganta hakan da ƙoƙarin gwamnati a fannin ilimi.
Shi ma Sakataren Ilimi na ƙaramar Hukumar Dala, Hon. Bala Magawata, ya ce ƙaramar hukumar na da ɗaruruwan makarantu, kuma kulawar gwamnatin jihar ta taimaka wajen samar da kayan koyo da koyarwa fiye da yadda ake samu a baya.
Ya bayyana cewa samar da waɗannan kayan na ƙarfafa gwiwar malamai da ɗalibai. Ya kuma yaba wa gwamnan kan umarnin biyan kuɗin jarrabawar sauya mataki daga firamare zuwa ƙaramar sakandare, domin ɗalibai su ci gajiyar wannan dama ba tare da biyan kuɗin ba.
Bala Magawata ya ce shugaban ƙaramar Hukumar Dala na daga cikin waɗanda ke bin umarnin gwamnan wajen biyan kuɗin jarrabawar sauya mataki (Transition Eɗamination) domin a ba ɗalibai damar ci gaba da karatu.
A nasa jawabin, Sakataren Ilimi na ƙaramar Hukumar Wudil, Ibrahim Idris Indabo, ya ce an samu gyare-gyare da gina sababbin gine-ginen makarantu a ƙaramar hukumar.
Ya yaba wa shugaban Hukumar Ilimi Bai ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB), Alhaji Abba Yusuf, da sauran masu ruwa da tsaki kan gudummawar da suke bayarwa wajen bunƙasa ilimi.
Ya kuma yabawa shugaban ƙaramar Hukumar Wudil, jagororin siyasar yankin da sauran masu kishin ci gaban ƙaramar hukumar kan gudummawa da haɗin kan da suke bayarwa wajen inganta harkokin ilimi.
