Atiku, Obi da wasu ’yan adawa ba su da mafita sai ƙiyayya – Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zargi jam’iyyun adawa da gabatar wa ’yan Nijeriya da saƙonnin ƙiyayya maimakon samar da mafita ga ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta. Ya kuma buƙaci masu zaɓe da su ƙi amincewa da abin da ya bayyana a matsayin saƙonnin yaƙin neman zaɓe masu rarrabuwar kai.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin babban taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Kaduna, inda ya kare ƙoƙarin gwamnatinsa na magance yunwa da talauci, tare da neman goyon bayan ’yan Nijeriya domin samun wa’adi na biyu.

Shugaban ƙasar, wanda ya ƙalubalanci jam’iyyun adawa kan sukar da suke yi wa gwamnatinsa, ya ce suna fushi ne saboda ba su da wata mafita mafi kyau da za su gabatar wa ’yan Nijeriya.

“Abokan hamayyarmu suna fushi ne saboda suna yaudararku. Ba su da abin da za su ba ku face ƙiyayya. Mu kuwa muna da wadata, daidaito, ci gaba, farfaɗowa da damammaki. Ina tabbatar muku da hakan,” inji Tinubu.

Ya kuma yi watsi da sukar da ’yan adawa ke yi kan yunwa da talauci, yana mai cewa waɗanda suke magana a yanzu kan matsalolin su ne suka haddasa su, yayin da gwamnatinsa ke ƙoƙarin magance su.

“Na ji abokan hamayyata suna magana kan yunwa da talauci. Wa ya haddasa su? Su ne. Su ne suka haddasa yunwa. Su ne suka haddasa talauci. Mu kuma muna ƙoƙarin kawar da su,” in ji shi.

Tinubu ya buƙaci ’yan Nijeriya da kada su bari saƙonnin yaƙin neman zaɓen ’yan adawa su ruɗe su, inda ya kira ga magoya bayansa da su kasance cikin shiri da sanya ido yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓe na gaba.

“Ku yi hankali. Ku sa ido a kansu. Kada ku bari su yi muku ƙarya,” ya faɗa wa mahalarta taron.

Shugaban ƙasar ya kuma roƙi masu zaɓe da su goyi bayan APC a dukkan matakan zaɓe, ciki har da zaɓen shugaban ƙasa, gwamnonin jihohi, ’yan Majalisar Tarayya da na majalisun dokokin jihohi. Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen samar da wadata da ci gaba.

Tinubu ya gode wa al’ummar Kaduna bisa halartar taron da suka yi da yawa, sannan ya sake jaddada alƙawarinsa na samar da kyakkyawar makoma ga ’yan Nijeriya a ƙarƙashin jagorancinsa.

By ukarofi

Leave a Reply