APC za ta yi kamfen kan ci gaban tattalin arziki da sauye-sauyen da ta kawo – Idris

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Jam’iyyar APC za ta yi kamfen ɗin zaɓen 2027 ne bisa nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ta samu a fannin bunƙasa tattalin arziki da sauya rayuwar ’yan Nijeriya cikin shekaru uku da rabi da suka gabata.

Idris ya bayyana hakan ne ranar Litinin, yayin jawabinsa a wajen ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan jihar da APC ta gudanar a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Ya ce: “Gaskiyar magana ita ce, gwamnatin APC ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sauya tattalin arzikin Nijeriya da rayuwar al’ummar ƙasar. Za mu yi kamfen ne bisa nasarorin da shugaban ƙasa ya samu cikin shekaru uku da rabi da suka gabata.”

Ministan ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar da sauran jam’iyyu za su yi fafutukar kayarwa, yana mai cewa ayyukan shugaban ƙasa da gwamnonin jam’iyyar sun sanya ta cikin yanayin neman ƙuri’un jama’a domin samun nasara a zaɓen 2027.

Idris ya kuma bayyana farin cikinsa na kasancewa cikin majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da kuma ta Jihar Neja, tare da yabawa Gwamna Mohammed Umaru Bago bisa naɗa shi cikin tsarin gudanar da kamfen ɗin.

Da yake ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen mai mambobi 525, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana cewa jihar za ta samar wa Shugaba Tinubu ƙuri’u sama da miliyan biyu a zaɓen mai zuwa.

Ya ce jam’iyyar za ta mayar da hankali kan wayar da kan jama’a da tattara goyon baya daga tushe, wato daga matakin ƙananan rassan jam’iyya har zuwa matakin jiha.

Gwamnan ya bayyana cewa tsarin yaƙin neman zaɓen ya ƙunshi rassan jam’iyya da jami’an siyasa da aka naɗa, yana mai cewa yawan mambobin tsarin ya haura 100,000 a tsawon shekaru.

By ukarofi

Leave a Reply