2027: Taron Arewa maso Yamma ya nuna ƙarfin APC – Haruna Wakili

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano kuma ɗan asalin ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Haruna Kabiru Wakili, ya bayyana taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da miƙa tutoci ga ’yan takarar gwamna na shiyyar Arewa Maso Yamma da aka gudanar a Kaduna, a matsayin babbar nasara da ke nuna karɓuwar APC a zukatan al’umma.

Hon. Wakili ya ce yadda dubban mutane suka fito daga jihohi daban-daban domin halartar taron, har suka cika wurin da aka gudanar da shi, ya tabbatar da amincewa da gamsuwar jama’a da manufofi da ayyukan jam’iyyar APC a faɗin ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa ɗimbin magoya bayan APC da suka fito daga Jihar Kano domin halartar taron, shaida ce karara ta goyon bayansu ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sauran ’yan takarar sanata da na Majalisar Wakilai. Ya ce suna shirye su ba da cikakken goyon baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

“Idan aka yi la’akari da irin ayyukan raya ƙasa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa, tun daga fannin ilimi, samar da ruwan sha, kiwon lafiya, gina hanyoyi, har zuwa tallafa wa matasa maza da mata domin su dogara da kansu, wannan babbar nasara ce da kowa ya gani,” in ji shi.

Hon. Wakili ya kuma yaba da kyakkyawan wakilcin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mai wakiltar Kano ta Arewa, yake yi. Ya ce ayyukansa na zahiri a fannonin ilimi, noma da tallafa wa ci gaban al’umma sun wuce Kano ta Arewa kaɗai, domin sun shafi Jihar Kano baki ɗaya.

Haka kuma, ya bayyana cewa sauran zaɓaɓɓun wakilan APC a matakai daban-daban na ci gaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar al’umma.

A ƙarshe, Hon. Haruna Kabiru Wakili ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa ’yan takarar APC goyon baya da haɗin kai. Ya kuma buƙace su da su tabbatar sun karɓi katin zaɓe, yana mai cewa katin zaɓen shi ne muhimmin kayan aiki da za su yi amfani da shi wajen tabbatar da nasarar ’yan takararsu a zaɓe mai zuwa.

By ukarofi

Leave a Reply