Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Kuɗi kuma mai Kula da Tattalin Arzikin Nijeriya, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa wasu ’yan Nijeriya na kashe kuɗin da ya kai kashi 120 cikin 100 na kuɗin shigarsu wajen sayen abinci, lamarin da ke tilasta musu karɓar bashi ko dogaro da ’yan uwa domin samun abin da za su ci.
Oyedele ya bayyana hakan ne yayin wani taro a cibiyar nazarin harkokin siyasa ta Chatham House da ke Landan, babban birnin Birtaniya, inda ya ce wani binciken da gwamnati ta gudanar ya nuna cewa kuɗin da wasu iyalai ke kashewa wajen sayen abinci ya zarce kuɗin shigarsu. Ya ce, “A gaskiya, mun gudanar da wani bincike da ya nuna cewa wasu iyalai na kashe har kashi 120 cikin 100 na kuɗin shigarsu wajen sayen abinci. Ta yaya mutum zai kashe kashi 120 cikin 100 na kuɗin shigarsa? Sai dai ya karɓi abinci a bashi kafin aarshen wata.”
Ministan ya kuma bayyana cewa duk da cewa yawan marasa aikin yi a Nijeriya ya kai kusan kashi biyar cikin 100, har yanzu sama da rabin al’ummar ƙasar na rayuwa cikin talauci. A cewarsa, wannan na nuna cewa akwai mutane da ke da ayyukan yi, amma har yanzu ba sa iya biyan buƙatunsu na yau da kullum. “Wannan ya kamata ya faɗakar da mu kan wani abu. A matsayina na mai tsara manufofin gwamnati, ba zan zauna kawai in ce babu matsalar rashin aikin yi ba. Muna da mutanen da suke aiki, amma har yanzu suna cikin talauci,” inji shi.
Oyedele ya danganta tsananin matsin tattalin arzikin da iyalai ke fuskanta da hauhawar farashin abinci, wanda a cewarsa ba ya raguwa cikin sauri kamar yadda hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka gaba ɗaya ke raguwa. Ya ce hauhawar farashin abinci ta kai kashi 19.6 cikin 100 a watan Satumba.
Ya bayyana cewa raguwar hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya ba ta nufin cewa farashin kayan abinci da jama’a ke amfani da su kullum ya ragu da irin wannan sauri ba. “Farashin kayayyaki gaba ɗaya na raguwa da sauri fiye da farashin kwandon kayan abinci da ya ƙunshi tumatir, garri da wake. Wannan kuwa yana ƙara faɗaɗa giɓin da ke tsakanin masu hali da marasa hali,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Daidaituwar tattalin arziki ba ta da wata ma’ana sosai ga uwa wadda har yanzu ba ta iya samun kuɗin sayen abincin da za ta ciyar da iyalinta.”
Ministan ya kuma ce Nijeriya ba ta sanya haraji kan man fetur, yana mai cewa matsin da iyalai ke fuskanta wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum ya samo asali ne daga matsalolin da suka daɗe suna addabar tattalin arzikin ƙasar, ba wai harajin man fetur ba. Ya lissafa ƙarancin amfanin gona da manoma ke samu, dogaro da noman damina kawai, lalacewar amfanin gona bayan girbi, ƙarancin wuraren adana amfanin gona, matsalolin sufuri da tsadar jigilar kayayyaki, da kuma rashin tsaro a yankunan noma a matsayin manyan abubuwan da ke haddasa tsadar abinci.
A matsayin misali, Oyedele ya ce har kashi 60 cikin 100 na tumatir kan lalace bayan girbi, abin da ke nuna irin asarar da ake yi a harkar noma sakamakon rashin ingantattun hanyoyin adanawa da jigilar amfanin gona. Dangane da matakan da gwamnati ke ɗauka domin magance matsalar, ministan ya ce ana zuba jari a fasahar noma, samar da ban-ruwa domin ba manoma damar yin noma a duk shekara, inganta wuraren adana amfanin gona da kuma sauƙaƙa wa ƙananan manoma samun rance.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta kuma fara bayar da tallafin kuɗi kai tsaye ga iyalai ta hanyar wani shirin tallafin kuɗi da ya riga ya isa ga gidaje sama da miliyan 10. Oyedele ya ce ana aika kuɗin tallafin ta hanyoyin zamani na lantarki, yayin da ake tantance waɗanda za su amfana da shirin ta amfani da Lambobin Shaidar ɗan ƙasa (NIN), domin rage yiwuwar karkatar da kuɗin ko kai su ga waɗanda ba su cancanta ba.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati na ba da fifiko ga harkar noma da kuma ayyukan tattalin arziki da galibi ake samarwa da amfani da su a cikin gida, waɗanda ba su dogara sosai da cinikayyar ƙasashen waje. A cewarsa, waɗannan fannoni biyu ne ke ɗaukar kashi 81.4 cikin 100 na ’yan Nijeriya masu aikin yi.
Ya ce manufar gwamnati ita ce bunƙasa waɗannan fannoni cikin sauri fiye da yadda tattalin arzikin ƙasar ke bunƙasa baki ɗaya, domin ƙara kuɗin shigar jama’a tare da rage dogaro da tallafin kuɗi kai tsaye a hankali.
