Wata mata mai suna Mary Christiana Oga ta rasu bayan wata turereniya da ta tashi yayin rabon kayan tallafi a ƙaramar hukumar Ogoja ta Jihar Kuros Riba.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba ta tabbatar da mutuwar matar, inda ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin Alhamis, 22 ga Oktoba, 2026, a yayin wani shirin tallafa wa jama’a da matar gwamnan jihar da tawagarta suka halarta.
A cewar rundunar, taron ya samu halartar jama’a da dama, waɗanda suka yi ta ƙaruwa yayin da ake raba kayan tallafin.
Yayin da mutane ke tururuwa domin samun nasu, sai aka samu turereniya wadda ta jefa mahalarta cikin haɗari.
Binciken da jaridar Leadership ta gudanar ya nuna cewa an ceto mata biyu daga wurin da lamarin ya faru, sannan aka garzaya da su Babban Asibitin Ogoja domin samun kulawar likitoci. Sai dai ɗaya daga cikinsu ta rasu bayan isar da ita asibitin.
An bayyana sunan mamaciyar a matsayin Mary Christiana Oga, ’yar garin Imaje da ke ƙaramar hukumar Yala ta jihar. Ita kuwa ɗayar matar da ta tsira daga lamarin ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin kulawar likitoci.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba, Ajo Geoffrey Ordue, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamaciyar tare da yi wa wadda ta tsira fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Kwamishinan ya jaddada muhimmancin tsara yadda ake kula da dandazon jama’a, samar da isassun matakan tsaro da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin masu shirya taruka domin kauce wa irin waɗannan munanan abubuwa.
Rundunar ’yan sandan ta ce tana nazarin yadda lamarin ya faru, yanayin turereniyar da kuma matakan da aka ɗauka wajen kula da jama’ar da suka halarci taron.
Ta kuma buƙaci al’umma su kwantar da hankalinsu tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba har sai an kammala bincike.
Lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan haɗarin tarukan rabon tallafi idan aka kasa tsara yadda mutane za su shiga, karɓar kayayyaki da ficewa cikin tsari.
Hukumomi kan buƙaci masu shirya irin waɗannan taruka su tabbatar da akwai isasshen sarari, ma’aikatan kula da taro da matakan gaggawa domin kare rayukan mahalarta.
