Gwamnatin Jigawa ta musanta zargin bai wa Rarara da Triple R gidaje kyauta

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Jihar Jigawa ta musanta zargin cewa ta bai wa fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, da mambobin ƙungiyar Triple R gidaje kyauta a sabon rukunin gidajen Danmodi da ke garin Ringim, tana mai cewa an gina gidajen ne domin samar da matsuguni ga al’ummar jihar masu cika ƙa’idojin mallakar su.

Rikicin ya fara ne bayan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda aka danganta da Rarara da mambobin ƙungiyar Triple R, inda aka yi magana kan aikin samar da gidaje da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta gudanar. Bidiyon ya jawo martani daga wasu ‘yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta, waɗanda suka fara tambayar ko an ware wa mawaƙin da abokan aikinsa gidaje daga cikin aikin da aka gina da kuɗin jama’a.

Sai dai, Dady Ringim, wani mai taimaka wa gwamnan ta fuskar kafafen sadarwa na zamani, ya yi watsi da wannan fahimta. Ya bayyana cewa maganganun da aka danganta da ƙungiyar ba su tabbatar da cewa gwamnan ya ba su gidaje kyauta ba, yana mai cewa abin da suke yi shi ne tallata ayyukan ci gaba da gwamnatin ta gudanar.

A cewarsa, an gina rukunin gidajen Danmodi ne a ƙananan hukumomi 27 na jihar, domin samar da gidaje ga ‘yan ƙasa waɗanda suka cika sharuɗɗan mallakar su. Ya ƙara da cewa tallata aikin gidajen wani ɓangare ne na bayyana ayyukan gwamnati, kamar na ilimi, hanyoyi, kiwon lafiya da noma.

Sai dai bayanin gwamnatin bai hana ci gaba da muhawara kan lamarin ba. Zakari Kafin Hausa, tsohon mai taimaka wa gwamnan kuma ɗan takarar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Auyo/Kafin Hausa a zaɓen 2027, ya nuna damuwa kan zargin ware gidajen ga mawaƙan siyasa, musamman ganin cewa aikin na iya kasancewa an samar da shi ne da kuɗin jama’a.

Zakari ya yi tambayoyi kan yadda ake gudanar da shirin gidajen, tare da sukar wasu matakai da ya ce suna buƙatar ƙarin bayani daga gwamnatin jihar. Matsayinsa ya ƙara ruruta muhawarar da ta taso kan wanda ya cancanci cin gajiyar shirin da kuma yadda ake tabbatar da adalci wajen raba gidajen.

A nasa ɓangaren, Ringim ya kare gwamnatin Namadi, yana mai cewa ayyukan da take gudanarwa ne ya kamata su zama ma’aunin tantance yadda take mulki, ba zarge-zarge da ake yaɗawa ba tare da cikakken bincike ba. Ya kuma buƙaci ‘yan siyasa da sauran jama’a su riƙa tantance bayanai kafin su yaɗa su.

By ukarofi

Leave a Reply