Ba don Tinubu ba da Buhari bai mulki Nijeriya ba – Abba Bichi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Bichi, Abubakar Abubakar, ya yi kira ga al’ummar Arewa da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, domin rama alherin da ya ce ya yi wa marigayi Muhammadu Buhari wajen samun nasarar zaɓen 2015.

Abba Bichi ya bayyana hakan ne ranar Litinin a yayin taron masu ruwa da tsaki da ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na mazabar Bichi a jihar Kano.

Ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya zama shugaban ƙasa bayan ya sha faɗuwa a zaɓukan da suka gabata, don haka lokaci ya yi da Arewa za ta nuna godiya ta hanyar zaɓen Tinubu karo na biyu.

ɗan majalisar ya kuma ce masu zargin gwamnatin Tinubu da nuna ƙiyayya ga Arewa ba sa faɗin gaskiya, yana mai cewa ayyukan raya ƙasa da aka amince da su a yankin sun nuna kishin shugaban ƙasar.

Ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki na siyasa a Kano ta Arewa sun shirya tattara aƙalla ƙuri’u miliyan ɗaya domin Tinubu a zaɓen 2027, daga cikin masu rajistar zaɓe kusan miliyan 1.3 da ke yankin.

A nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya buƙaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen da su tabbatar da nasarar dukkan ’yan takarar APC, tare da guje wa duk wani abu da zai kawo tashin hankali.

Haka kuma, Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamna na APC a Kano, Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya bukaci mambobin jam’iyyar su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan matasa da sauran magoya baya, tare da kiyaye zaman lafiya kafin da bayan zaɓe.

By ukarofi

Leave a Reply